Jerin Ministoci: Tinubu Na Kokarin Maye Gurbin Abiru Da Ambode a Matsayin Sanatan Lagas
- An rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu na yunkurin dawo da Akinwunmi Ambode, tsohon gwamnan jihar Lagas, a harkar siyasa
- An ce shugaban kasar na duba yiwuwar mayar da Ambode sanata mai wakiltan Lagas ta gabas yayin da za a yi wa wanda ke kan kujerar dannar kirji da mukamin minista
- A cewar wata majiya a fadar shugaban kasa, idan har abun ya yi aiki, Ambode zai samu mukami imma a fadar shugaban kasa ko a jiha
FCT, Abuja - An rahoto cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana duba yiwuwar dawowa da tsohon gwamnan jihar Lagas, Akinwunmi Ambode, a harkokin siyasa.
Punch ta rahoto cewa, majiyoyi da ke da masaniya kan ci gaban sun bayyana cewa shugaban kasar na duba yiwuwar ganin tsohon gwamnan ya zama sanatan Lagas ta gabas yayin da za a yi wa wanda ke rike da mukamin a yanzu, Tokubo Abiru, dannar kirji da mukamin minista.
Ambode zai samu mukami imma a fadar shugaban kasa ko a jiha
Ambode shine gwamnan jihar Lagas na uku tun bayan fara jumhuriyya ta hudu. Ya gaji Babatunde Fashola amma shugabannin siyasar jihar suka hana shi zarcewa a karo na biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugabannin siyasa a jihar sun maye gurbin Ambode da Babajide Sanwo-Olu. Tun daga lokacin ba a sake jin doriyar Ambode ba har sai kwanan nan da Tinubu ya zama shugaban kasa, wanda ya hadu da Fashola, Ambode da Sanwo-Olu a makon jiya a Lagas.
A ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, Ambode ya ziyarci Tinubu a fadar Villa, inda ba a bayyana cikakken bayanin ganawar tasu ba.
Yadda Tinubu ke shirin dawowa da Ambode harkar siyasa
Sai dai kuma wata majiya a fadar shugaban kasar ta bayyana cewa akwai alamu da ke nuna cewa Ambode na iya samun mukami imma a jihar ko fadar shugaban kasa idan abubuwa suka tafi daidai a bangarensa.
Daga cikin shirye-shiryen shine nada shi ya zama sanata mai wakiltan Lagas ta gabas, yayin da Abiru, wanda shine a kai yanzu zai zama minista a karkashin shugaban kasa Tinubu.
Majiyar ta ce:
"Akwa yiwuwar cewa tsohon gwamnan zai samu mukami imma a fadar shugaban kasa ko a jihar idan har abubuwa suka tafi daidai a bangarensa."
Yadda Bincike da Zargin Sata Zai Jawo Na Hannun Daman Tinubu Su Rasa Ministoci
A wani labarin, mun ji cewa wasu ‘yan siyasa da ke tunanin kusancinsu da Bola Ahmed Tinubu zai jawo su samu kujerar Minista, za su sha mamaki ba da dadewa ba.
Wani bincike da Punch ta gudanar, ya nuna cewa shugaban kasa zai dogara da rahoton da jami’an tsaro su ka gabatar masa wajen nada Ministoci.
Asali: Legit.ng