Peter Obi Ya Yi Magana Kan Shirin Sake Tsayawa Takara a Shekara 2027
- Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), ya musanta rahotannin cewa zai sake tsayawa takara a shekarar 2027
- Obi ya nuna ɓacin ransa kan rahotannin karyan inda ya yi bayanin cewa ba a yi wannan tattaunawar da shi ba inda ta nan aka samo rahotannin
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya sake nanata jajircewarsa wajen yin magana kan abubuwan da suka shafi ƙasar nan ta hannun amintattun jaridu da kafafen sadarwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya musanta rahotannin da ke cewa ya fara shirin sake tsayawa takara a shekarar 2027.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya nesanta kansa daga rahotannin a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter ranar Asabar, 15 ga watan Yuli.
Gwamnan PDP Ya Tona Asiri, Ya Faɗi Yadda Jiharsa Ke Asarar Biliyan N10 Duk Ranar Litini Saboda Abu 1
Ya bayyana cewa rahotannin zuƙi ta malle ce kawai waɗanda suka samo asali daga hirar da ba a yi da shi ba.
Ɗan takarar na jam'iyyar LP ya kuma musanta cewa ya yi magana kan naɗe-naɗen da gwamnatin tarayya ta ke shirin yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Na lura cike da takaici sabuwar hanyar da ta ɓullo inda ake ƙirƙiro rahotannin ƙarya a cikin hirarrakin da ba a yi dani ba."
"Abubuwa biyu da suka faru kwanan nan sun haɗa da na cewa na ce na fara shirin tsayawa takara a shekarar 2027 a wata hira da Arise TV wacce kwata-kwata ba a yi ta ba."
"Ɗayan kuma shi ne kan batun maganar da na yi akan naɗe-naɗen da gwamnatin tarayya za ta yi. Dukkanin rahotannin shaci faɗi ne kawai. Abin takaici siyasar mu ta taɓarɓare ta koma yanzu an mayar da yin ƙarairayi a kafafen watsa labarai ta zama sana'a."
Zan ci gaba da magana kan abubuwan da suka shafi ƙasa - Peter Obi
Obi ya sake nanata jajircewarsa kan yin magana akan lamuran da suka shafi ƙasar nan ta hanyar sahihan kafafen watsa labarai da shafukan sada zumunta.
Ɗan siyasar wanda haifaffen jihar Anambra ne ya bayyana cewa ba zai damu kansa da ƴan baranda ba.
"Mayar da hankali na da na tafiyar 'Obidient' ba zai kauce ba daga kan ainihin manufar mu ta samar da sabuwar Najeriya wacce mu ka yi amanna cewa zai yiwu."
Tinubu Ya Gano Hanyar Wargaza LP
A wani labarin kuma, wani babban jigo a jam'iyyar PDP ya bankaɗo shirin Shugaba Tinubu na ba wani babban jigo a jam'iyyar LP muƙamin minista.
Daniel Bwala ya bayyana hakan zai kawo rabuwar kai a jam'iyyar ta LP da magoya bayanta.
Asali: Legit.ng