Matawalle Ya Gabatar da Shaidu 19 Domin Kwace Mulki Daga Dauda Lawal a Zamfara

Matawalle Ya Gabatar da Shaidu 19 Domin Kwace Mulki Daga Dauda Lawal a Zamfara

  • Bello Matawalle ya gabatar da shaidu 19 gaban Kotun sauraron karar zaben gwamnan jihar Zamfara
  • Bayan sauraron shaidun, Kotun zaɓen ta ɗage zaman ƙarar zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2023
  • Ɗaya daga cikin shaidun kuma baturen zaɓen karamar hukumar Maradun ya bayyana yadda aka hana shi faɗin sakamakon da ya tattara

Zamfara - Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben gwamnan jihar Zamfara ta ɗage zama zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2023, kamar yadda jaridar Tribune online ta ruwaito.

Kotun ta ɗage zaman ne bayan tsohon gwamna, Bello Matawalle, ya gabatar da shaidu 19 domin gamsar da Kotu kan ƙarar da ya kalubalanci nasarar Dauda Lawal.

Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara.
Matawalle Ya Gabatar da Shaidu 19 Domin Kwace Mulki Daga Dauda Lawal a Zamfara Hoto: Bello Matawalle
Asali: UGC

Matawalle, ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen 18 ga watan Maris, ya garzaya Kotun zaɓe ya kalubalanci nasarar gwamna Dauda Lawal na jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Tona Asiri, Ya Faɗi Yadda Jiharsa Ke Asarar Biliyan N10 Duk Ranar Litini Saboda Abu 1

Tsohon gwamnan ya ce zaben da aka gudanar cike yake da kura-kurai da maguɗi, bisa haka ya buƙaci Kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara saboda ya samu mafi yawan halastattun kuri'u.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma roƙi Kotun ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta hanzarta ba shi sabon satifiket ɗin shaidar cin zaɓe, kamar yadda Punch ta rahoto.

Abinda shaidun suka faɗa wa Kotun zaɓen Zamfara

Yayin ci gaba da sauraron karar ranar Jumu'a, lauyan Matawalle, Usman Sule SAN, ya gabatar da shaidu 19 bisa jagorancin baturen zaben karamar hukumar Maradun, Dakta Ahmad Kainuwa.

Kainuwa ya bayyana wa Kotu takardar sakamakon zaɓen da ya tattara daga kowace gunduma a wani ɓangaren shaidun da Matawalle ya gabatar.

Ya ce kiri-kiri INEC ta hana shi miƙa wannan sakamako kuma ta sanya shi ya sanar da sakamakon zaben da ya tattara daga shafin yanar gizo na INEC.

Kara karanta wannan

Dirama: Wani Shaida da PDP Ta Gabatar Ya Bata Kunya a Gaban Kotu, Ya Bayyana Gaskiya

Ya faɗa wa Kotun cewa sakamakon zaɓen da ya tattara daban da wanda ya gani a shafin hukumar zaɓe.

Amma jami'an hukumar suka umarce shi da ya bayyana wanda yake a Fotal ɗin INEC domin shi ne sahihi.

Bugu da ƙari, Kainuwa ya faɗa wa Kotun cewa an samu tashin hankali a karamar hukumar Maradun kuma DPOn yan sanda ya tilasta masa dakatar da tattara sakamako.

Bayan kammala sauraron shaidun, Alkalin kotun mai shari'a Cordelia Ogadi ta ɗage zaman zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2023.

Gwamnonin Kudu da Shugabannin Igbo Zasu Gana da Tinubu Kan Muhimmin Abu 1

A wani rahoton na daban Gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas da shugabannin Inyamurai zasu gana da shugaba Tinubu kan matsalar da ta addabe su.

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya bayyana haka ga masu ɗauko rahoton gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaban Tinubu a Aso Villa.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Dage Sauraron Karar Doguwa Da Gwamnatin Jihar Kano Kan Muhimmin Dalili 1 Rak

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262