Tsohon Shugaban Banki Daga Kudu Maso Yamma Na Iya Zama Ministan Kudin Tinubu, Majiya
- Shugaban kasa Tinubu na duba yiwuwar ba wani tsohon shugaban wani bankin zamani daga kudu maso yamma mukamin ministan kudi
- Ana sa ran mutumin, wanda ya shiga harkar siyasa a 2020 kuma babban Akanta zai zamo cikin masu ilimin fasaha da shugaban kasar zai ba mukami
- Tinubu na da burin barin tsohon tsarin nade-naden mukmai da kuma hada tawagar kwararru domin magance matsalolin kasar, kamar yadda wata majiya ta bayyana
Abuja - Yayin da yan Najeriya ke jiran jerin ministocin shugaban kasa Bola Tinubu, wani rahoto ya yi nuni ga wanda za a iya nadawa a matsayin ministan kudi.
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, mutumin da ake tunanin baiwa wannan mukami na minista ya kasance wani tsohon shugaban wani bankin zamani daga kudu maso yamma.
Mutumin wanda ya shiga harkar siyasa a 2020 yana daya daga cikin masu ilimin fasaha da ake ganin Tinubu zai nada a matsayin ministoci.
Legit.ng ta tattaro cewa mutumin ya kasance dan kungiyar FCA ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Nigerian Tribune ta nakalto majiyar na cewa:
"Shugaban kasar na sane da bukatar barin tsohon tsari wajen nada ministoci. Ya nuna hakan a jihar Lagas cewa shi mutum ne mai hazaka.
"Ku tabbata yana tattara tawaga mai karfi don tunkarar matsaloli a kasar."
Jerin ministoci: Yan Najeriya na jiran mutanen da Tinubu zai zaba
Shugaban kasa Tinubu zai nada minista daga jihohi 36 da babban birnin tarayya domin taimaka masa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada ministoci 44 inda wasu jihohin suka samu minitoci bibbiyu.
El-Rufai, Fayode da George sun ce ba za su amsa tayin Tinubu ba ko da ya gabatar masu da kujerun ministoci
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu manyan yan siyasa na ci gaba da kamun kafa don shiga majalisar Shugaban kasa Bola Tinubu.
Sai dai kuma, wasu fitattun yan siyasa kamar su tsohon gawmanan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose da kuma tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP mai adawa, Bode George sun ce ko da an zo masu da tayin kujerar ba za su karba ba.
Asali: Legit.ng