Ana Shirin Kinkimo Ƙanin Tsohon Gwamna, a ba shi Minista a Gwamnatin Tinubu

Ana Shirin Kinkimo Ƙanin Tsohon Gwamna, a ba shi Minista a Gwamnatin Tinubu

  • Kungiyar Save Nigeria Movement ta ce Austine Umahi ake so ya zama Minista daga jihar Ebonyi
  • Shugaban SNM ya ce tsohon Gwamna kuma Sanata mai-ci yana so a ba ‘danuwan shi mukami
  • Austine Umahi yana cikin jagororin APC a Ebonyi, shi ya rikewa ‘danuwansa takarar Sanata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wata kungiya mai suna Save Nigeria Movement (SNM) tayi kira ga Bola Ahmed Tinubu da ya yi hattara da tsohon Gwamna, Dave Umahi.

Wannan kungiya ta SNM ta aiko da jawabi zuwa ga Legit.ng, ta na cewa Sanata David Umahi ya na neman kakaba ‘danuwansa ya zama Minista.

SNM mai ikirarin ceto al’ummar Najeriya tayi magana ne a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja ta bakin shugabanta, Rabaren Solomon Semaka.

Bola Tinubu a Ebonyi
Bola Tinubu wajen kamfe a Ebonyi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ban da rashin adalci - SNM

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gano Hanyar Wargaza LP, Zai Ba Na-Hannun Daman Peter Obi Kujerar Minista

Rabaren Solomon Semaka yana so idan Bola Tinubu ya tashi nada Ministocinsa, ya tafi da kowa domin samu zaman lafiya a yankin kudu maso gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan aka baris ai yadda Umahi su ka yi a Ebonyi, SNM ta na ganin rikici zai iya barkewa a jihar wanda ko a yanzu abubuwa su na neman su tafasa.

A cewar Semaka, ganin cewa rade-radi sun yi yawa, ya kamata a ankarar da al’umma game da bada sunan Austine Umahi da aka yi ya zama Minista.

Zargin da ake yi wa Sanatan Kudancin jihar Ebonyi shi ne ya kai sunan ‘danuwansa na jini kuma jigo a APC domin ya samu kujerar Ministan tarayya.

Kungiyar SNM ta zargi Umahi da maida sha’anin mulki ya zama tamkar gadon danginsu.

An rahoto Rabaren din yana cewa duk da kowa yana da damar rike mukami, bai dace mutanen da ke kiran ayi adalci, su kawo abin da zai zama zalunci ba.

Kara karanta wannan

Yadda APC Ta Hana Tinubu Kudi a Lokacin Kamfe In Ji Mataimakin Shugaban Jam’iyya

Jawabin shugaban SNM

"Bincikenmu ya nuna mana Austine Umahi kani ne ga tsohon Gwamnan Ebonyi wanda ya rika juya madafan iko a shekaru takwas na ‘danuwansa.

Idan za a tuna, bayan tsohon Gwamna Ebonyi ya shafe wa’adi biyu daf da zaben 2023, sai ya fito neman tikitin APC, amma Shugaba Tinubu ya doke shi."

- Solomon Semaka

Kungiyar ta ce akwai alamar tambaya a kan yadda Umahi ya zama Sanata bayan ya nemi takarar shugaban kasa, abin da ya jawo Ann Angom ta je kotu.

LP za ta samu Minista?

Mu na da labari Bola Ahmed Tinubu yana so ya wargaza manyan ‘yan adawarsa daga jam’iyyar LP, zai nada wani daga cikinsu a matsayin Minista.

Daniel Bwala ya yi wannan magana ta bar magoya bayan LP a duhu, yanzu ana ta tunanin Farfesa Pat Utomi ko Dr. Doyin Okupe zai yi watsi da Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng