Gwamnan Jigawa Umar Namadi Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 16
- Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya rantsar da sabbin kwamishinoni 16 a gidan gwamnatinsa da ke Dutse
- Namadi ya roƙi sabbin kwamishinonin da su sanya tsoron Allah a zuƙatansu wajen sauke nauyi da amanar mutanen Jigawa
- Ya ce mazauna jihar na yi wa gwamnatinsa kyakkyawan zaton cewa zata kawo musu canji a walwalar rayuwarsu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jigawa state - Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 16 da ya naɗa a majalisar zartarwan gwamnatinsa.
Leadership ta ce yayin basu rantsuwar kama aiki, Gwamna Namadi ya buƙaci kwamoshinoni su yi aiki bisa tsoron Allah, gaskiya da riƙon amanar al'umma da kuma sauke haƙƙi.
Sabbin kwamishinonin sun kama aiki gadan-gadan bayan gwamna Namadi ya zaɓe su kuma majalisar dokokin jihar Jigawa ta tantance su kamar yadda doka ta tanada.
Da yake jawabi a wurin bikin rantsar da kwamishinonin, gwamna Namadi ya ce ya kula sosai wajen zakulo mutanen duba da gaskiyayarsu, iya aiki, sadaukarwa da rashin son kai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan ya ce:
"A matsayina na sabon gwamna ina buƙatar kwararrun mutane da suka san hannunsu, waɗanda zasu taimake ni wajen cika alƙawurran da na ɗauka da ɗaga darajar Jigawa zuwa babban matsayi."
"Kuma Allah SWT bisa rahamarsa mara karewa ya zaɓe ku, dan Allah ina roƙon karku bari na ji kunya."
"Yana da muhimmanci na sanar da ku cewa wannan gwamnatin tana buƙatar aiki tuƙuru, sadaukarwa, biyayya da kuma tsantsar aiki babu nuna son kai."
Ya bayyana cewa mutanen Jigawa suna sa ran gwamnatinsa zata zo da tsaruka da shirye-shirye, waɗanda zasu inganta rayuwarsu ta yau da kullum.
Jerin sunayen kwamishinonin da ma'aikatun da zasu jagoranta
Sunayen Gwamnonin APC, PDP Da A Halin Yanzu Ke Kokarin Kwaton Kansu A Kotu Kan Matsalar Takardun Karatu
1. Aminu Ahmad AK - Ma'aikatar kasuwanci
2. Hajiya Hadiza Abdulwahab - Ma'aikatar harkokin mata
3. Injiniya Gambo S. Malam - Ma'aikatar ayyuka
4. Farfesa Hannatu Sabo Muhammad - Ma'aikatar kuɗi
5. Auwalu Sankara - Ma'aikatar ayyuka na musamman
6. Babangida Gantsa - Ma'aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziƙi
7. Honorabul Ibrahim Garba - Ma'aikatar albarkatun ruwa
8. Dakta Isah Yusuf Chamo - Ma'aikatar ilimin manyan makarantu, kimiyya da fasaha.
9. Dakta Lawan Yunusa Danzomo - Ma'aikatar ilimi
10. Dakta Muhd Abdullahi Kainuwa - Ma'aikatar lafiya
11. Muhd Garba MK - Ma'aikatar ƙananan hukumomi
12. Muhammad Alhassan - Ma'aikatar filaye
13. Dakta Nura Ibrahim Dandoka - Ma'aikatar muhalli
14. Alhaji Muttaka Namadi - Ma'aikatar noma
15. Sagiru Musa Ahmad - Ma'aikatar yaɗa labarai
16. Musa Adamu Aliyu - ma'aikatar shari'a.
Aminu Majeh, ɗan cikin garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa da yawan mutanen jihar sun yi murna da mutanen da gwamna ya naɗa a matsayin kwamishinoni.
Ya ce duk da mafi akasarin kwamishinonin sun yi aiki a gwamnatin baya amma ya sa basira wajen dawo da tsoffin waɗanda sun yi aiki tukuru ga al'umma a zamanin Badaru.
Ya ce:
"Wallahi na tabbatar Dan Modi (Umar Namadi) ba sa'an yaro bane, aiki kawai yazo, da tawansu tsoffin kwamishinoni ne ya mayar. Sun san aikin zasu cu gaba daga inda suka tsaya."
Shugaba Tinubu Ya Gana da Sabon Mukaddashin Shugaban EFCC a Villa
A wani labarin na daban kuma Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da masu almundahana ta ƙasa (EFCC).
Wannan ganawa ta ranar Laraba na zuwa ne makonni hudu bayan Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga matsayin shugaban EFCC.
Asali: Legit.ng