Tinubu Ya Fara da Kyau Amma Tun Farko na San Babu Inda Buhari Zai Je - Dattijon Arewa

Tinubu Ya Fara da Kyau Amma Tun Farko na San Babu Inda Buhari Zai Je - Dattijon Arewa

  • Tanko Yakasai yana ganin hasashen da ya taba yi a game da Muhammadu Buhari ya tabbata gaskiya
  • Dattijon bai cikin wadanda su ka amince da tsohon shugaban kasar, har gobe bai canza ra’ayi a kan shi ba
  • Yakasai ya ce tun da Buhari ya bar mulki, ya kamata masu goyon bayansa su fadi cigaban da ya kawo

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A wata hira ta musamman da aka yi da Tanko Yakasai, ya yi magana game da mulkin Muhammadu Buhari da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Sun ta fara da tambayar Alhaji Tanko Yakasai kan kamun ludayin Bola Ahmed Tinubu, ya kuma shaida cewa mafi yawan ‘yan Najeriya na farin-ciki.

Yabo ga Gwamnatin Tinubu

"Kowa ya yarda za a shawo kan manyan matsalolin Najeriya a mulkin Tinubu. Na yi imani cewa da gaske yake yi, bambancinsa da sauran shugabanni kenan.

Kara karanta wannan

Yadda APC Ta Hana Tinubu Kudi a Lokacin Kamfe In Ji Mataimakin Shugaban Jam’iyya

Tanko Yakasai
Tanko Yakasai ya yi magana kan Buhari da Tinubu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu yana da tsari, ba cin karo ya yi da mulki ba, yanzu ya samu damar da zai aiwatar da tsarinsa. Ina farin ciki da yadda yake gudanar da abubuwa a yanzu.

- Tanko Yakasai

Kama Bawa da Emefiele

A hirar da aka yi da dattijon, an tabo batun cire tallafin fetur da kuma cafke shugabannin EFCC da CBN, a nan ya nuna abin da ake bukata shi ne a tafi kotu.

Yakasai bai goyon bayan wani da aka kama, amma ya ce kyau a bar kotu tayi shari’a da gaskiya.

Na san aabu Abin da Buhari zai tabuka

Ganin Muhammadu Buhari ya kammala mulkinsa, an samu damar tambayar tsohon Kwamishinan na Kano a lokacin mulkin soja game da gwamnatin bayan.

Yakasai mai shekara 91 ya ce matsyarsa ba ta taba canzawa, tun tashin farko ya fadawa Duniya shugaba Buhari ba zai iya ba, kuma a cewarsa haka aka kare.

Kara karanta wannan

Bude Iyakokin Najeriya: Shugaban Kwastam Ya Yi Magana Bayan Zaman Farko Da Tinubu

"Bai dace ku yi mani tambayar nan ba domin kun san matsaya ta. Ban taba tsammanin abu dabam ba, a karshe ba su yi abin da ya wuce wanda nake sa rai ba.
Kun yi hira da ni a baya kuma na fada maku ka da ayi tunanin wata mu’ujiza daga gwamnatin Buhari."
Yanzu ya gama mulkinsa, ya rage ga magoya bayansa su fito su fada mana irin nasarorin da ya samu. Tun farko ban yi tunanin zai yi nasara, na san ba zai yi ba.

- Tanko Yakasai

Ministocin da za a nada

A lokacin mulkin Muhammadu Buhari na biyu, jihar Bauchi ta samu kujeru biyu a Gwamnatin tarayya. Wannan karo an ji labari za a samu yamutsi.

Tsakanin magoya bayan APC irinsu Isa Yuguda, Mohammed Pate, Musa Babayo da Yusuf Tugga, kowa ya ci burin gwaninsa ya zama Ministan tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng