Darusa 4 Da Aka Fahimta Daga Nasarar Tinubu Da Shettima a Zaben 2023, El-Rufai

Darusa 4 Da Aka Fahimta Daga Nasarar Tinubu Da Shettima a Zaben 2023, El-Rufai

  • Nasir El-Rufai yana da ra’ayin cewa zaben shugaban kasa da aka yi, ya koyawa mutane hankali
  • Tsohon Gwamnan na Kaduna ya ce yanzu an fahimci adalcin Musulmai da Bola Tinubu ya hau mulki
  • Zaben 2023 ya kunyata masu ci da addini da kokarin tunzura al’umma a cewar Malam El-Rufai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce galabar APC ta koyawa masu bakar kiyayya ga sauran addini wasu muhimman darusa.

Malam Nasir El-Rufai ya na ganin Bola Ahmed Tinubu ya rufe bakin abokan adawa tun wajen nadin mukamansa, Premium Times ta kawo labarin.

Tsohon Gwamnan ya yi wannan bayani ne da ya halarci bikin kaddamar da littafin da aka buga domin karrama shugaban MURIC, Ishaq Akintola.

Nasir El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai a lokacin yana mulki Hoto: @GovKaduna
Asali: Facebook

El-Rufai ne wanda ya gabatar da jawabi a wajen taron da aka shirya domin Farfesa Ishaq Akintola, ya yi magana kan abin da ya shafi sha’anin siyasa.

Kara karanta wannan

‘Yan Siyasa Sun Raba Hankalin Tinubu, Za a Rasa Wanda Zai Zama Minista Daga Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daina duba addini ko kabila

Da yake magana, El-Rufai ya ce ya kamata wajen zabe, mutanen Najeriya su rika zaben shugabannin da su ka san yadda za a magance matsaloli.

A wajen yin hakan, tsohon Ministan na Abuja ya ce bai dace a rika la’akari da addini ko kabila ba, ya na ganin a daina kawo addini wajen harkar siyasa.

Darasin farko a wurinsa da aka koya daga zaben shi ne an yi maganin ‘Yan kudu da ke ganin mutanen Arewa su na da kwadayin mulki ko ta halin ƙa- ƙa.

Ina masu ci da addini a siyasa

Nasarar Tinubu da shan kunyan Peter Obi, ya zama na uku, ya karyata masu hasashen bogi da wadanda su ka maida mimbarin coci wajen kamfe.

Jaridar ta rahoto El-Rufai yana cewa a zaben bana aka fahimci halacci da cika alkawarin ‘yan siyasar Arewa, su ka sallama mulki ya komawa Kudu.

Kara karanta wannan

Jami’an Gwamnati Sun Dura Gareji, An Yi Awon Gaba da Motocin Tsohon Gwamna

Duk da an ji tsoron tikitin Tinubu-Shettima saboda duka ‘yan takaran musulmai ne, ‘dan siyasar ya ce Kiristoci sun fi samun mukamai a gwamnati mai-ci.

Ko da shugaban kasa da mataimakinsa Musulmai ne, El-Rufai ya ce ba za ayi wa wadanda ba Musulmai rashin adalci a karkashin jagorancin musulmi ba.

Tinubu ya kiyayi Uzodinma

A makon nan aka ji labari Ikenga Imo Ugochinyere Ikeagwuonu wanda ‘Dan majalisar tarayya ne, ya tona alakar Gwamnan Imo da Shugaban APC.

‘Dan majalisar ya ce Hope Uzodinma ya yaki Bola Tinubu a APC, ya so Ahmed Lawan ya samu takara a APC saboda ya zama mataimakin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng