An Shawarci Tinubu Da Kar Ya Kuskura Ya Bai Wa Masu Neman Mukami Ido Rufe Dama a Gwamnatinsa

An Shawarci Tinubu Da Kar Ya Kuskura Ya Bai Wa Masu Neman Mukami Ido Rufe Dama a Gwamnatinsa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna na lokacin mulkin soja, kanar Abubakar Umar Dangiwa ya shawarci Tinubu kan masu neman mukami
  • Ya ce bai kamata Shugaban Tinubu ya tsaya ci gaba da sauraron irin wadannan muanen da ke nuna maitarsu a fili wajen neman mukami ba
  • Ya gargadi Tinubu kan bai wa tsoffin gwamnoni mukamai, wadanda ya ce mafi yawancinsu sun talauta lalitar jihohinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - An shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya kiyayi ba da mukami ga wasu da aka bayyana da masu neman mukami ko ta halin kaka.

Tsohon gwamnan Kaduna na mulkin soja, Kanar Abubakar Dangiwa Umar mai ritaya ne ya bayyana haka ranar Litinin din da ta gabata kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa.

Dangiwa ya shawarci Tinubu kan mutanen da ya kamata ya hana mukami
Dangiwa ya fadawa Tinubu kar ya saurari masu neman mukami ido rufe. Hoto: Leadership
Asali: UGC

Dangiwa ya shawarci Tinubu hana tsoffin gwamnoni mukamai

Kara karanta wannan

Yadda Sabon Tsarin Shugaba Tinubu Ya Tilasta Gwamnonin PDP Biyu Rage Yawan Ma'aikatu a Jihohinsu

Dangiwa ya shawarci Tinubu, musamman kan ba da mukamai ga tsofaffin gwamnonin jihohi, wadanda ya ce mafi yawa daga cikin sun talauta jihohinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma ce wasu daga cikinsu sun bar jihohin nasu da bashi mai tarin yawa, tare da jefa jihohin nasu cikin rikicin addini da na kabilanci kafin saukarsu daga mulki.

Dangiwa ya kara da cewa Tinubu ba zai so a rika dauke masa hankali ba a lokacin da yake kokarin dawo da kasar kan turbar da ta dace.

Dangiwa ya soki gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari a baya

Dangiwa ya kasance mai fada a ji a kasar kuma sanannen mai sukar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda shugaban kasar ya tafiyar da mulkin kasar tsawon shekaru takwas.

A shekarar 2021, ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da nuna rashin kwarewa wajen tafiyar da al’amura daban-daban a kasar kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jerin Ministoci: Sunayen Tsaffin Gwamnoni Da Suka Taba Yin Minista Da Za Su Iya Sake Zama Ministoci

Ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari, kan abinda ya kira bata lokaci da take yi kan masu fafutukar a raba kasa maimakon mayar da hankali kan matsalar ‘yan ta’adda da suka addabi wasu yankunan kasar.

Yadda sabbin tsarukan Shugaba Tinubu suka tilastawa gwamnoni 2 rage yawan mukamansu

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan yadda tsarukan da Shugaba Tinubu ya zo da su sanya wasu gwamnoni biyu rage yawan ma’aikatun jihohinsu.

Cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi na daga cikin abubuwan da suka tilasta gwamnonin jihohin Taraba da Zamfara sauya tsarukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng