Sakataren APC Ya Jero Irin Mutanen da Shugaban Kasa Zai Dauko Su Zama Ministoci
- Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta bayyana abin da ya hana a iya nada Ministoci har yanzu
- Iyiola Omisore ya shaida cewa Bola Tinubu ya na shawara ne tukuna kafin ya kafa Gwamnatinsa
- Ana ta jita-jita, Sakataren na APC ya nesanta kan shi da sunayen wadanda ake cewa za a ba mukamai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja- A jiya Iyiola Omisore ya kawo karshen jita-jitan da ke yawo game da nadin sababbin Ministoci da za su yi aiki a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Da aka yi hira da shi a tashar Channels a ranar Talata, Sanata Iyiola Omisore ya shaida cewa har yanzu Bola Ahmed Tinubu bai fitar da Ministoci ba.
Sakataren na jam’iyyar APC na kasa ya ce abin da ya jawo hakan shi ne shugaban kasar bai gama tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan batun ba.
‘Dan siyasar ya ce Bola Tinubu yana tuntubar jam’iyya da sauran wadanda ke da ta-cewa game da nadin mukaman, kafin fito da jerin Ministocin kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gaskiyar sunayen da ke yawo
Tribune ta ce Omisore ya yi watsi da rade-radin da ake tayi, ana yawo da sunayen wasu a matsayin wadanda za su zama Ministoci a gwamnati mai ci.
A matsayinsa na Sakataren APC, ya ce mutanen Najeriya su shirya ganin Ministoci na dabam, wadanda su ka san aiki kuma su ka sa aikin a gabansu.
Wannan karo idan an tashi zakulo wadanda za a kafa gwamnati da su, Sanata Omisore ya ce za a dauko Ministoci ne da za su maida hankali ga aiki.
Tsohon mataimakin Gwamnan ya kara da cewa za a lalubo mutanen da za su aiwatar da manufofin Tinubu wadanda kan haka jama’a su ka zabe shi.
Abin da Iyiola Omisore ya fada
"Ba a fito da sunayen ba tukuna. Mu na tattaunawa, ana ta yanke shawara, har zuwa awanni hudu da su ka wuce, mun yi zama da shi (Tinubu)
Mu na so a samu gwamnati ta dabam da za ta cika burin ‘Yan Najeriya. ‘Yan Najeriya sun yi suna wajen rade-radi, ni babu ruwa na da wannan."
- Iyiola Omisore
The Nation ta rahoto Omisore yana cewa adadin Ministocin ba za su wuce 37 zuwa 43 ba. Kowace jiha za ta samu guda, sai a samu kari daga kowane yanki.
Dawowar Tinubu daga Bissau
A baya an samu labari Femi Gbajabiamila da tsofaffin Gwamnoni su ka tarbo Bola Ahmed Tinubu a tashar jirgin sama da ya dawo daga taron ECOWAS.
Mai girma shugaban Najeriyan ya na tare da irinsu Abdullahi Umar Ganduje wanda ake ta surutai a kan yiwuwar ya zama Minista a gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng