"Na Cancanci Zama Ministan Tinubu", Tsohuwar 'Yar Takarar Shugaban Kasa Ta Bayyana Dalilanta
- Ƴar takarar da ta janyewa Shugaba Tinubu takara a lokacin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, Ibinabo Joy Dokubo ta ƙalubalanci shugaban ƙasar
- Dokubo tace ta cancanci muƙamin minista domin saka mata kan namijin ƙoƙarin da ta yi wajen samun nasarar jam'iyyar APC da shugaba Tinubu
- Dokubo ta bayyana kanta a matsayin mai ƙwarewa ta fanni biyu saboda ita matashiya ce kuma mace mai tarihi mai kyau a baya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kusa cike wa'adin da yake da shi domin bayyana ministocinsa kamar yadda doka ta tanada.
Ana ci gaba da kamun ƙafa domin samun muƙamin minista inda har Ibinabo Joy Dokubo, ƴar takara ɗaya mace tilo a zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa, ta bayyana cewa ta cancani samun minista a gwamnatin Tinubu, The Sun ta rahoto.
Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1
Ƴar takarar shugaban ƙasa ta APC ta ƙalubalanci Shugaba Tinubu
Dokubo ta ƙalubalanci shugaban ƙasar da ya saka wa ƴaƴan jam'iyyar da suka yi aiki domin nasararta da muƙamin ministoci da muƙamai masu gwaɓi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jigon a jam'iyyar APC ɗin ta bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Talata, 11 ga watan Yuli, inda ta ƙara da cewa ta yi huɓɓasa sosai wajen tabbatar da nasarar shugaban ƙasa Tinubu.
Ta kuma bayyana cewa yakamata a saka mata saboda ƙokarin da ta yi da kujerar minista, cewar rahoton The Cable.
Dalilin da ya sanya shugaba Tinubu yakamata ya ba ni minista
Wani ɓangare na kalaman Dokubo na cewa:
"Bayan ƙokari na wanda ake gani da wanda ba a gani ba da suka samar da nasara a wajen zaɓen Shugaba Tinubu, ni mace ce mai halin kirki, cancanta da ƙware wa da sanannnen tarihi mai kyau."
Wata Kungiya Ta Ankarar Da Hukumomi Kan Shirin Ganduje Na Sulalewa Daga Kasar Nan, Ta Bada Shawarar Abun Da Za Ayi Masa
Ta kuma bayyana kanta a matsayin wacce ta cancanci samun minista saboda ita mace ce kuma matashiya.
Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade
A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake sanar da yin wasu sabbin naɗe-naɗe masu muhimmanci.
Shugaban ƙasar ya naɗa Olusegun Dada a matsayin mai taimaka masa kan kafafen sada zumunta da Abdulaziz Abdulaziz a matsayin mai taimaka masa na musamman a ɓangaren jaridu.
Asali: Legit.ng