Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Amince Da Amfani Da Hausa Wajen Gudanar Da Al'amuranta

Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Amince Da Amfani Da Hausa Wajen Gudanar Da Al'amuranta

  • Majalisar Dokokin jihar Bauchi ta sanar da sanya harshen Hausa cikin yarukan gudanar da lamuranta
  • Kakakin majalisar, Honarabul Abubakar Y Suleiman ne ya bayyana hakan ranar Talata
  • An bayyana cewa kashi 90% na al'ummar jihar Bauchi, suna amfani da harshen Hausa wajen gudanar da al'amuransu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Bauchi - Majalisar dokokin jihar Bauchi, ta sanya harshen Hausa baya ga turanci cikin yarukan gudanar da harkokinta.

Kakakin majalisar, Honarabul Abubakar Y Suleiman ne ya sanar da hakan a zauren majalisar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Shira, Honarabul Auwal Hassan ne ya gabatar da wannan ƙudirin a ranar Talata.

Za a rika amfani da Hausa a majalisar jihar Bauchi
Majalisar Bauchi ta amince a rika amfani da harshen Hausa cikin al'amuranta. Hoto: Muhammad Abba S. Fawa
Asali: Facebook

Dalilin sanya harshen Hausa cikin lamuran majalisar ta Bauchi

Da yake gabatar da ƙudirin, Hassan ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar da cewa za a riƙa gudanar da abubuwan gwamnati da ma waɗanda ba na gwamnati ba cikin harshen Turanci.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Abba Gida-Gida Ya Mayar Da Sheikh Daurawa Kan Mukaminsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai ya ce wata doka da majalisar jihar ta yi a shekarar 2017, ta bai wa majalisar ikon gudanar da harkokinta cikin harshen Turanci ko wani ɗaya daga cikin yarukan da ake da su a jihar.

Ya ƙara da cewa, harshen Hausa ne sama da kashi 90% na al’ummar jihar Bauchi ke amfani da shi wajen sadarwa, wanda da hakan ne ya ba da shawarar a ƙara da shi baya ga Turanci a matsayin yare na biyu da za a riƙa amfani da shi.

Karo na biyu kenan ana gabatar da ƙudurin a majalisar

Da yake nuna bayansa, Honarabul Musa Wakili Nakwada, wanda ke wakiltar mazaɓar Bogoro, ya yabawa abokin aikinsa kan ƙudirin, inda ya bayyana cewa ya taɓa gabatar da ƙudirin a majalisa ta 9 da ta shuɗe.

Kara karanta wannan

Za a rina: Gwamna ya umarci farfesan halayyar dan Adam ya zauna da dalibar da ta kara sakamakon JAMB

A yayin da kakakin majalisar ya gabatar da ƙudirin domin jin ra'ayoyin sauran jama'a, sun amince da shi ba tare da wani tarnaƙi ba.

An yabawa Gwamnan jihar Bauchi Saboda gyara bangaren lafiya

A wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa, an yabawa gwamnan jihar Bauchi bisa irin ƙoƙarin da ya yi na inganta harkokin kiwon lafiya.

Kwamishinan lafiya na riƙon ƙwarya a jihar, Aliyu Babayo Gamawa ne ya bayyana hakan a wajen wani taro a jihar.

Ya ƙara da cewa ɓangaren lafiya a jihar ya samu ci gaba sosai tun daga lokacin da Bala ya karɓi ragamar mulkin jihar a 2019.

Gwamnan Bauchi ya bai wa alhazan jiharsa maƙudan kuɗaɗe a Saudiyya

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto da ke cewa, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya gwangwaje alhazan jihar su 3,000 da kyautar kuɗaɗe riyal 300 kowanensu.

Mukhtar Gidado, mai ba gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai ne ya bayyana hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng