Shettima Na Ganawa Da Abbas, Kalu Da Wasu Shugabannin Majalisar Wakilai

Shettima Na Ganawa Da Abbas, Kalu Da Wasu Shugabannin Majalisar Wakilai

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya yi kira ga Majalisar Wakilai ta bai wa Tinubu goyon baya
  • Ya bayyana hakan ne a yayin da shugabannin majalisar ta wakilai suka ziyarce shi a gidan gwamnati
  • Ya kuma yi kira ga sabbin shugabannin da su bai wa kakakin majalisar haɗin kai wajen gudanar da ayyuka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Rahoton da ke zuwa mana na nuni da cewa mataimakin shugaban ƙasa kashim Shettima, na wata ganawa ta sirri da shugabannin Majalisar Wakilan Najeriya a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ne ya jagoranci sauran shugabannin majalisar zuwa taron da Shettima kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilan, Benjamin Kalu na cikin mahalarta taron.

Shettima ya nemi goyon bayan Majalisar Wakilai ga gwamnatinsu
Shettima ya nemi Majalisar Wakilai ta bai wa Tinubu goyon baya. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Shettima ya nemi majalisa ta bai wa Tinubu goyon baya

Kara karanta wannan

Dalla-Dalla: Yadda Dokar Ta Ɓacin da Tinubu Ya Ayyana Kan Samar da Abinci Zata Taimaka Wa Yan Najeriya

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi kira ga shugabannin Majalisar Wakilai da su marawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu baya na kawo sauyi a kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Mista Shettima, shugaban kasar ya kuduri aniyar sake fayyace ma’ana da manufar shugabanci na zamani kamar yadda ya fara taɓa ko ina tun daga ranar farko.

Shettima ya ce duba da yanayin da ƙasar take ciki, ya zama wajibi a haɗa ƙarfi da ƙarfe ba tare da la'akari da banbance-banbancen jam'iyya, addini ko ƙabilanci ba.

Ya ce abinda ya haɗa 'yan ƙasar ya fi abinda ya rabasu, domin kuwa tun a farko ƙasa ɗaya ce al'umma ɗaya kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

Shettima ya nemi sabbin shugabannin majalisa sun bai wa kakakin majalisar haɗin kai

Shettima ya jaddada goyon bayan Tinubu ga majalisar, inda ya ƙara da cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa duk tsofaffin ‘yan majalisar ne.

Kara karanta wannan

Shugaban Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Batun Samar da Abinci a Najeriya, Ya Bada Sabon Umarni

Shettima ya yaba da sabon jagorancin da aka samu a majalisar, inda ya roke su da su bai wa kakakin majalisar goyon baya, domin yi wa ƙasa aikin da ya kamata.

A kalamansa:

“Muna alfahari da ku, muna roƙon ku da ku yi aiki tare saboda yanzu mun wuce matakin siyasa; yanzu muna cikin tsarin mulki.

Majalisar Wakilai ta dakatar da ƙarin kuɗin makarantu da aka yi

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan dakatar da batun ƙarin kuɗaɗen manyan makarantun Gwamnatin Tarayya da Majalisar Wakila ta yi.

Majalisar ta ce ƙarin kuɗin makarantar ka iya kawo cikas ga karatun da yawa daga cikin ɗaliban da iyayensu ke da ƙarancin abin hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng