Gwamnonin PDP Na Shirin Yin Wata Ganawa Mai Muhimmanci a Abuja, Za a Sasanta Manyan Jiga-Jigan Jam’iyya
- Halin da kasar ke ciki a yanzu ya zama babban abun damuwa ga jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP)
- Gwamonin da aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar PDP sun shirya wani taron gaggawa kan haka
- Kungiyar gwamnonin PDP za ta yi taron gaggawa a ranar Talata, 11 ga watan Yuli, a Abuja, taro na farko bayan zaben 2023
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kungiyar gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shirya wani taron gaggawa don tattauna halin da kasar ke ciki.
An shirya yin taron ne a ranar 11 ga watan Yuli, a Abuja kuma shine na farko da kungiyar za ta yi bayan babban zaben 2023.
Dalilin da yasa gwamnonin PDP za su yi taron gaggawa
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa, ana sa ran gwamnonin za su tattauna halin da kasar ke ciki, manufofin sabuwar gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da rikicin da ya ki ci yaki cinyewa a jam'iyyar tun bayan zaben fidda dan takarar shugaban kasa a bara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyoyin sun kuma bayyana cewa watakila gwamnonin na PDP su kafa wani kwamiti domin yin kokari da magance rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar da kuma sulhunta manyan 'ya'yan jam'iyyar da suke aikin da ya saba ra'ayin jam'iyyar.
Jerin ministoci: Dalilin da yasa Wike ya cancanci shiga majalisar Tinubu, Fayose ya yi bayani
A wani ci gaban kuma, Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu na bukatar mutum irin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a majalisarsa.
Fayose ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli, yayin wata hira da gidan talbijin na Channels a wani shirin dare.
A cewar Fayose, ya zama dole shugaban ‘yan tafiyar G5 din ya samu kujera a gwamnati mai-ci saboda irin rawar da ya taka waje kifar da PDP.
Mukhtar Shehu Shagari ya fice daga PDP bayan shekaru 24
A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon ministan noma da albarkatun ruwa, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Tsohon mataimakin gwamnan na jihar Sokoto, Shagari ya yi murabus daga jam'iyyar PDP kuma ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Asali: Legit.ng