Bayan Rigimar Majalisa, Rikicin Kuɗi Zai Kunno Kai Tsakanin Shugabannin APC

Bayan Rigimar Majalisa, Rikicin Kuɗi Zai Kunno Kai Tsakanin Shugabannin APC

  • Alamu na nuna kamar babu jituwa tsakanin shugabannin jam’iyya na kasa da ragowar ‘Yan NWC
  • Ana zargin Abdullahi Adamu da hana sauran shugabannin APC ganin rahoton binciken kudi da aka yi
  • Watakila hakan ne ya yi sanadiyyar dakatar da taron NEC da jam’iyyar APC tayi niyyar yi a makon nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Abubuwa ba su tafiya daidai a jam’iyyar APC har ta kai an fara jita-jita cewa an samu sabani tsakanin shugabanni na kasa a majalisar NWC.

Ana zargin cewa Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya na kokarin boye binciken kudi da aka gudanar, wannan labari ya fito a jaridar Punch.

Majiyoyi barkatai su ka shaida za ayi rikici a jam’iyyar APC idan Sanata Adamu ya ki ba sauran ‘yan NWC damar ganin rahoton binciken kudi da aka yi.

Kara karanta wannan

Obasanjo, Buhari, IBB Da Lokuta 9 Da Shugaban Najeriya Ya Zama Shugaban ECOWAS

Shugabannin APC
Shugabannin APC da 'Yan PGF a Sakatariya Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Adamu kadai yake rawarsa?

Wani a cikin shugabannin APC na kasa ya yi hira ta musamman da jaridar, ya kuma zargi Adamu da jagorantar jam’iyyar ba tare da sauran ‘yan NWC ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda Salihu Lukman ya fada, shi ma wannan ya ce tsohon Gwamnan na jihar Nasarawa bai tafiya da sauran ‘yan kwamitinsa wajen shugabanci.

A cewar ‘dan kwamitin, har zuwa yanzu, ba a gabatarwa majalisarsu da rahoton binciken da aka yi kan yadda kudi su ka shiga ko fita daga jam’iyya ba.

Za a yi zaman NEC babu batun kudi?

Muddin NWC ba ta samu rahoton ba, ‘dan siyasar ya ce bai ga ta yadda za a dauki takardar kuma a iya gabatar da ita a wajen taron majalisar koli ta NEC.

Rahoton ya kuma nuna da karfe 1:00 na ranar Litinin ne shugaban APC na kasan zai yi zama da duka shugabannin jam’iyya na reshen jihohi a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata: Majalisa Za Tayi Binciken Yadda Aka Saida Kadarorin Gwamnati

Wani jigo a jam’iyyar ya ce Adamu zai yi amfani da zaman ne domi samun karin goyon baya.

... an fasa yin zaman sai makon gobe

Hakan yana zuwa ne a lokacin da ake fitar da sanarwa cewa an dakatar da taron majalisar NEC wanda jam’iyyar APC ta shirya ranakun Talata da Laraba.

Legit.ng Hausa ta fahimci an fasa zaman ne kwatsam bayan an sanar da lokaci da wuri. Bayanan da aka samu a Twitter ya ce taron ya koma 18 da 19 ga Yuli.

Da aka tuntube shi a matsayin Mai magana da yawun jam’iyya, Felix Morka ya shaida cewa bai san halin da ake ciki ba domin babu sanarwar da aka fitar.

“Ina goyon bayan Wike”

Idan Asiwaju Bola Tinubu ya ga cancantar wani daga cikin ‘Yan kungiyar G5, an ji labari Ayo Fayose ya ba su shawarar su shiga cikin gwamnatin APC.

‘Dan siyasar ya ce tsohon Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya na da baki, kuma ya san kan aiki, saboda haka ya ce Najeriya na bukatar wani shu’umi irinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng