Rarara Ya Fi Ganduje Dacewa Tinubu Ya Bai Wa Mukami a Gwamnatinsa, Dan APC Bashir Kabo Ya Yi Bayani
- Wani ɗan jam'iyyar APC a jihar Kano, Bashir Shata Kano, ya ce bai kamata Tinubu ya bai wa Ganduje minista ba
- Ya ce kamata ya yi Shugaba Tinubu ya bai wa Dauda Kahutu Rarara muƙamin a maimakon Ganduje
- Ya ƙara da cewa Ganduje da muƙarrabansa ne suka yi sakacin da ya janyowa APC faɗuwa zaɓe a jihar Kano
Kano - Wani ɗan jam'iyyar APC Bashir Shata Kabo, ya bayyana cewa Rarara ya fi dacewa Shugaba Tinubu ya bai wa muƙami ba Ganduje ba.
Ya bayyana hakan ne a hirarsa da gidan rediyon Freedom da ke Kano, a cikin shirin nan na Kowane Gauta.
Ya ce waƙar da Rarara ya yi ta yi matuƙar tasiri wajen zaɓar jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu a zaɓen da ya gabata.
Waƙar Rarara ta taimaka wajen zaɓen Tinubu da APC da aka yi
Ya kuma ce waƙar da Rararan ya yi ta taimaka wajen zaɓen ƙarin wasu kujerun da dama ƙarƙashin jam'iyyar ta APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shata ya ƙara da cewa sam bai dace Tinubu ya bai wa Ganduje muƙamin minista ba a gwamnatinsa.
Ya bayyana cewa Ganduje da muƙarabansa ne suka janyowa jam'iyyar APC faɗuwa a zaɓen da ya gabata a Kano, don haka bai kamata a ba ɗaya daga cikinsu kowace irin kujera ba.
Ya yi kira ga shugaban ƙasa Tinubu, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Adamu, da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ka da su yarda su bai wa Ganduje ko 'yan tawagarsa muƙami.
Ganduje da muƙarrabansa ba za su iya riƙe wata kujera ba
Shata ya ce waƙar da Rarara ya yi mai taken 'girmanka akwatinka' ta taka muhimmiyar rawa wajen zabar APC.
Ya kuma bayyana cewa yadda Ganduje da muƙarrabansa suka bari aka kayar da su a zaɓen da ya gabata, ya nuna cewa ba za su iya riƙe wata kujera yadda ya kamata ba.
Sannan Shata ya ƙara da cewa Rarara ya riga da ya zama ɗan jihar Kano, musamman in aka yi la'akari da irin gudummawar da ya bai wa 'yan jihar Kano.
Kotu ta dakatar da gayyatar da aka yi wa Ganduje
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta dakatar da hukumar PCACC daga gayyatar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.
Hukumar ta PCACC dai ta gayyaci tsohon gwamnan ne don ya amsa tambayoyi kan bidiyonsa na dala da take bincike a kai.
Asali: Legit.ng