Sheikh Gumi Ya Bayyana Manyan Dalilan Tinubu 2 Na Yin Ritayar Dole Ga Sama Da Manyan Sojoji 100
- Sheikh Ahmad Gumi, babban malamin addinin Muslunci na garin Kaduna, ya yi tsokaci kan naɗin sabbin shugabannin tsaro da Shugaba Bola Tinubu ya yi
- Gumi ya soki yadda kowace sabuwar gwamnati tun 1999 zuwa yau ke yi wa janar-janar na sojoji da yawa ritaya
- Gumi wanda shi ma tsohon janar ɗin soja ne, ya bayyana cewa irin hakan asara ce ga ƙasa da kuma ɓangaren tsaro
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Fitaccen malamin addinin Muslunci Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana cewa al'adar yi wa sojoji ritayar dole da sabbin gwamnatoci tun 1999 ke yi, ba aba ba ce mai kyau.
Gumi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tsokaci dangane da naɗe-naɗen shugabannin tsaro da Shugaba Tinubu ya yi, inda za a yi wa kwamandoji 100 ritayar dole.
Gumi ya bayyana illar yi wa sama da sojoji 100 ritayar dole
Gumi wanda shima tsohon janar ɗin soja ne, ya bayyana cewa bai kamata a yi wa sojoji masu tarin yawan irin haka ritaya ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gumi ya ce:
"Abin takaici ne matuƙa, abin baƙin ciki ne yadda muka rasa jami'an bayan horar da su, wasunsu sun samu horaswa a ƙasashen waje, inda aka kashe maƙudan kuɗaɗe don horar da su dabarun yaƙi na musamman."
Da yake zantawa da Trust TV, malamin ya danganta matsalar da wasu manyan batutuwa guda biyu da suka addabi hukumar sojojin. Ya bayyana matsalolin kamar haka:
Siyasantar da muƙamin shugabannin tsaro
Gumi ya bayyana cewa an siyasantar da muƙaman shugaban shugabannin tsaro, wanda kuma hakan ke janyo Najeriya asarar kuɗaɗe da kuma mutane masu basira.
Ya ce an sanya ƙabilanci, addini da ɓangaranci wajen naɗa ko cire shugabannin tsaro na ƙasa, inda ya bayyana cewa bai kamata a ringa yin hakan ba.
Tsarin al'adar gidan soja
Malamin ya kuma bayyana cewa al'ada ce ta gidan soja, cewa dole ne manyan sojoji su yi murabus a yayin da aka naɗa na ƙasa da su muƙamin shugaban sojoji na ƙasa.
A kalamansa:
“Tsarin muƙamin gidan soja bai ba da damar ƙaramin jami'i ya shuganci manyansa ba. Za a riƙa samu matsala wajen gudanar da ayyuka, don haka don haka dole ne a yi musu ritaya.”
Tsofaffin sojoji sun bai wa sabbin shugabannin tsaro shawarwari kan harkokin tsaro
Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a baya kan shawarar da manyan tsofaffin sojoji suka ba da kan yadda za a magance matsalar tsaro.
Manyan tsoffin sojojin sun ce yana da kyau sabbin hafsoshin tsaro su yi koyi da yadda magabatansu suka gudanar da ayyukansu ta hanyar duba nasarori da kurakuran da suka yi.
Asali: Legit.ng