Gwamna Dikko Radda Na Katsina Ya Naɗa Mataimaki Na Musamman Kan Harkokin 'Yan Gudun Hijira
- Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda, ya naɗa mataimaki na musamman kan harkokin 'yan gudun hijira a jihar
- Sakataren gwamnatin jihar, Akitek Ahmad Musa Dangiwa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba
- Gwamnan ya yi naɗin ne domin ganin an kula da mutanen da hare-haren 'yan bindiga ya raba da Mujallansu a faɗin jihar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Katsina - Gwamna jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya naɗa Alhaji Sa'idu Ibrahim Danja, a matsayin mataimaki na musamman kan 'yan gudun hijira na jihar.
Dikko ya naɗa Sa'idu ne domin kula da 'yan gudun hijra na jihar Katsina, waɗanda ta'addancin 'yan bindiga ya tilastawa barowa gidajensu da garuruwansu.
Wannan dai na ƙunshe ne a wata sanarwa da Legit.ng ta tsinkayo a shafin Fesbuk na Daraktan yaɗa labaran gwamnatin jihar, Isah Miqdad AD Saude.
Sanarwar naɗin ta fito ne ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, Akitek Ahmad Musa Dangiwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwa ta bayyana cewa naɗin na Saidu ya fara aiki ne daga ranar Larabar, 5 ga watan Yulin 2023 da muke ciki.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, an yi duba ne da gogewa da kuma sanin makamar aiki da Sa'idu Ibrahim ke da ita kafin naɗa shi muƙamin.
Gwamna Dikko Radda ya taya Sa'idu Ibrahim murna
Gwamna Radda ya taya Sa'idu murna ta wannan dama da ya samu, don bai wa jihar Katsina gudummawa wajen kula da waɗanda matsalar 'yan ta'adda ta shafa.
Wannan dai wani bangare ne na ƙudirin gwamnan wajen ganin ya magance ƙalubalen da mutanen da ayyukan ‘yan ta'adda ya raba da matsugunnensu a faɗin jihar, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Muhimman Alkawura 3
Gwamnan ya bayyana irin kwarin gwirwar da yake da ita kan Sa'idu wajen ganin jihar ta samu damar kulawa da waɗanda matsalar 'yan ta'addan ta shafa yadda ya kamata.
Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da mutane biyu a Katsina
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan mamakon ruwan sama da ya haifar da ambaliyar ruwan da ta yi sanadin rasa rayukan mutane biyu a Katsina.
Ambaliyar dai ta faru ne a daidai sabuwar gadar kurɗe ta kofar ƙaura da gwamnatin tsohon gwamnan jihar Aminu Masari ya gina.
Asali: Legit.ng