Gwamnan Kano Zai Sanya Idanu Kan Ayyukan Kwamishinoninsa Na Tsawon Wata 6
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya nada kwamitin da zai lura da kowane kwamishina da ya nada kan ayyukan da yake yi
- Gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin tabbatar da cewa kowane daga cikinsu ya yi abinda ya dace
- Abba ya kuma bayyana cewa za su sallami kwamishinonin da ba su yi kokari ba cikin wannan lokaci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana cewa watanni shida kowane kwamishina ke da su wajen nuna kwazon aikinsa.
Abba ya ce za su sanya ido a kan duka kwamishinonin a cikin watanni shidan farko, wanda daga nan ne za a yanke shawara kan a ci gaba da tafiya da mutum ko akasin haka kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wata Kungiya Ta Nemi a Gudanar Da Bincike Na Gaggawa Kan Yadda Gwamnan Zamfara Dauda Lawal Ya Tara Dukiyarsa
Abba ne zai jagoranci kwamitin sanya idanu kan ayyukan kwamishinonin nasa
Gwamnan ya bayyana cewa shi da kansa zai jagoranci kwamitin da zai rika sanya idanu kan ayyukan da kowane kwamishina yake gudanarwa a ma’ikatarsa cikin wannan lokaci da aka diba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya bayyana hakan ne ranar Talata, a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar da ya jagoranta a gidan gwamnati.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Hisham Habib ya bayyana cewa gwamnan ya fadawa kwamishinonin cewa an ba su mukaman ne bisa cancantarsu da kuma gogewa da suke da ita ta aiki.
Abba ya nemi kwamishinonin su yi aiki tukuru
Gwamnan ya kuma yi kira ga kwamishinonin da su yi aiki tukuru wajen ceto jihar Kano daga halin da gwamnatin baya ta jefa ta a ciki.
Daga karshe Abba ya godewa daukacin al’ummar jihar inda ya ba su tabbacin cewa nan da wani dan lokaci za su fara ganin sauye-sauyen da za su amfanesu kai tsaye kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne sabuwar gwamnatin ta Abba Gida Gida ta kaddamar da sabbin kwamishinoni a jihar.
Gwamnatin Kano ta sake dawo da bincike kan bidiyon dala na Ganduje
Legit.ng ta kawo muku rahoto a baya kan cewa hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano (PCACC), ta sake tado da batun bidiyon da aka ga Ganduje na karbar daloli yana sanyawa aljihu.
Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata a Kano.
Asali: Legit.ng