Bidiyon Dala: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano Ta Kaddamar Da Bincike Kan Ganduje

Bidiyon Dala: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano Ta Kaddamar Da Bincike Kan Ganduje

  • Hukumar Karbar Koke-Koke Da Yaki Da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano (PCACC), ta sake bude babin binciken kan tsohon gwamnan jihar
  • Hukumar ta zargi tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje da karbar daloli na cin hanci daga hannun ‘yan kwangila
  • Hukumar ta ce za ta hada kai da wasu hukumomi a yayin binciken don tabbatar da an kare kima da darajar jihar

Kano - Hukumar Karbar Koke-Koke Da Yaki Da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano (PCACC), ta kaddamar da bincike a hukumance kan tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, kan faifan bidiyonsa na karbar rashawa.

Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan ranar Talata a wata ganawa da manema labarai a Kano.

An sake tado da batun bincike kan bidiyon dala na Ganduje
An tado da sake bude babin bincike kan bidiyon dala na Ganduje. Hoto: Barr. Muhuyi Magaji Rimingado, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Rimingado ya sha alwashin dawo da bincike a kan bidiyon dala na Ganduje

Kara karanta wannan

Kotu Ta Ba Da Umarnin Tsare Tsohon Kwamishina Har Kwanaki 12 Kan Zargin Badakalar Biliyan 1

Daily Trust ta ruwaito cewa a makon da ya gabata ne shugaban hukumar ya sha alwashin sake tado da bincike kan bidiyon tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon da ake tuhumarsa da shi, wanda ya yadu a wani lokaci can baya, an ga Ganduje na karbar curin dalolin Amurka yana cusawa cikin aljihunsa.

An dai yi zargin cewa Ganduje ya karbi wadannan kudade ne daga hannun ‘yan kwangila, zargin da tsohon gwamnan ya musanta.

Rimingado, ya bayyana cewa hukumar ta fara gudanar da binciken a hukumance, kuma a halin yanzu tana nazari kan faya-fayen bidiyon.

Ya kuma bayyana cewa sun rubutawa hukumar EFCC takarda ta neman hadin kansu wajen Gudanar da binciken.

A rahoton jaridar Vanguard, Muhuyi ya bayyana cewa za su yi kokarin ganin cewa sun binciki bidiyon da kyau, saboda a cewarsa abu ne da ya shafi kima da darajar jihar Kano.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Gangwaje Alhazan Jihar Kano, Ya Ba Su Kyautar Miliyan 65

An kama kwamishinan Ganduje bisa zargin almundahanar naira biliyan daya

Muhuyi Magaji ya kuma tabbatar da kama wani tsohon kwamishinan a lokacin Ganduje, Injiniya Idris Wada Saleh, kan zargin almundahanar kudade da suka kai naira biliyan daya.

Ya ce tsohon kwamishinan ya yi wadakar naira biliyan daya ne gab da karshen gwamnatinsu, da sunan za a gyara wasu manyan hanyoyin jihar.

Ya kara da cewa an kuma kama babban sakatare na Hukumar Kula da Kayayyakin Jama’a (BPP), Mustapha Madaki Huguma, da kuma daraktan kudi, da daraktan bincike da tsare-tsare na hukumar ranar Litinin.

An nemi kotu ta hana EFCC bincikar tsohon gwamnan jihar Kano

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wani korafi da aka shigar a gaban kotu na neman ta dakatar da EFCC daga binciken ko gayyatar tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Tsohon Atoni janar na jihar Kano ne ya shigar da koken, inda ya bukaci an jira har lokacin da aka gama shari’a tsakanin Gandujen da Jaafar Jaafar na jaridar Daily Nigerian.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng