Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Shaidar Karatunsa Na Jami'ar Chicago
- Shugaba Tinubu ya kare kansa game da rudanin da ya dabaibaye batun karatunsa a gaban Kotun sauraron korafin zaɓe mai zama a Abuja
- Ta hannun lauyansa, shugaban kasan ya gabatar da takardun karatun da ya yi a jami'ar Chicago da ke ƙasar Amurka ranar Talata
- Wannan na zuwa ne yayin da Tinubu ya buɗe fagen kare kansa game da korafin PDP da Atiku Abubakar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar kwafin takardun karatunsa na jami'ar jihar Chicago ta ƙasar Amurka a gaban kotun zaɓe mai zama a Abuja.
Shugaba Tinubu ya gabatar da takardun ne a matsayin shaidar tabbatar da karatunsa a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen shugaban ƙasa ranar Talata, 4 ga watan Yuli.
The Nation ta rahoto cewa Tinubu ya fara kokarin kare kansa kan ƙarar da PDP da ɗan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar suka shigar.
Bola Tinubu ya gabatar da takardun ta hannun lauyansa, Chief Wole Olanipekun, tare da takardar da ya karɓa daga hannun ofishin jakadancin Amurka a Najeriya tun a shekarar 2007.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Takardar dai ta wanke Bola Tinubu daga zargin aikata kowane laifi a ƙasar Amurka, ya kuma gabatar da takardar da hukumar 'yan sandan Najeriya ta aike wa ofishin jakadancin Amurka don neman karin haske.
Tinubu ya gabatar da takardu 12 a gaban Kotun, wanda ya ƙunshi masu ɗauke da bayanan karatun da ya yi a jami'ar Chicago, waɗanda jami'ar ta ƙara tabbatar da sahihancinsu ranar 28 ga watan Yuni, 2023.
Sauran takardun da Tinubu ya gabatar a matsayin shaida
Bugu da ƙari, wanda ake ƙara ya gabatar da wasu kwafin takardu shida dangane da shige da fice da bayanan bizar tafiya-tafiyen Tinubu zuwa Amurka tsakanin 2011 zuwa 2021.
Idan baku manta ba a lokacin kamfe, tsagin adawa sun yi musun cewa shugaba Tinubu bai da shaidar karatu a jami'ar Chicago kamar yadda yake iƙirari.
Haka nan Atiku da PDP sun kafa hujja da wannan dalilin suka roƙi Kotu ta rushe nasarar da ya samu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Shugaban APC da Mambobin NWC Na Ganawa da Gwamnonin PGF a Abuja
A wani labarin na daban kuma Mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) sun shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC (PGF) a birnin tarayya Abuja.
Wasu majiyoyi daga cikin APC sun shaida cewa wannan zama zai tattauna batun taron masu ruwa da tsaki da majalisar ƙoli (NEC) mai zuwa.
Asali: Legit.ng