Shugaban APC, Mambobin NWC Suna Ganawa da Gwamnoni a Abuja

Shugaban APC, Mambobin NWC Suna Ganawa da Gwamnoni a Abuja

  • Mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) sun shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC (PGF) a birnin tarayya Abuja
  • Rahoto ya nuna cewa taron zai maida hankali kan shirye-shiryen manyan taruka biyu da ke tafe a mako mai zuwa
  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, mataimakansa na kudu da arewa da sauran jiga-jigai sun halarci zaman yau Talata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC ta ƙasa (NWC) na ganawa mai muhimmanci yanzu haka da shugabannin ƙungiyar gwamnonin APC (PGF) a Sakatariyar jam'iyya da ke Abuja.

Wasu majiyoyi daga cikin APC sun shaida cewa wannan zama zai tattauna batun taron masu ruwa da tsaki da majalisar ƙoli (NEC) mai zuwa, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Taron NWC da gwamnonin APC.
Shugaban APC, Mambobin NWC Suna Ganawa da Gwamnoni a Abuja Hoto: The Deputy Governor of Kaduna/Facebook
Asali: Facebook

Jam'iyyar APC ta shirya gudanar da taron shugabannin da suka hau karagar mulki a inuwarta ranar Litinin mai zuwa yayin da taron NEC zai biyo baya ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tajudeen Abbas Ya Bayyana Sunayen Sabbin Jagororin Majalisar Wakilan Tarayya Ta 10

Taron, wanda ya kunshi mambobin NWC karkashin jagorancin shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, shi ne na farko tun bayan zaɓen sabbin shugabannin ƙungiyar gwamnonin APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan baku manta ba gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya samu nasarar zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyya mai mulki (PGF).

Mahalarta taron sun haɗa da shugaban jam'iyya na ƙasa, Sanata Adamu, Sakatare, Sanata Iyiola Omisore; mataimakin shugaban jam'iyya (arewa), Sanata Abubakar Kyari, da mataimakin shugaba (kudu), Emma Enukwu.

Sauran sun haɗa da mataimakin sakatare na ƙasa, Barista Festus Fanuter; mataimakin shugaban jam'iyya (arewa maso yamma), shugaban matasa, shugabar mata da sauransu.

Jerin gwamnonin APC da suka halarci taron

Gwamnonin da aka hanga a wurin taron sun haɗa da, Hope Uzodinma (Imo), Yahaya Bello (Kogi), Abdulrahman AbdulRasak (Kwara); da Babajide Sanwo-Olu (Lagos).

Sauran su ne, Biodun Oyebanji (Ekiti); Rabaran Hyibcent Alia (Benuwai); Malam Dikko Raɗda (Katsina); Mai Mala Buni (Yobe) da kuma Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe).

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Zargi APC Da Yunkurin Shirya Ma Ta Makirci Kan Kujerar Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisar Dattawa

Mataimakiyar gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Balarabe, ta wakilci Malam Uba Sani a taron, kamar yadda ta wallafa a shafin Facebook.

Tajudeen Abbas Ya Bayyana Sunayen Sabbin Shugabannin Majalisar Wakilan Tarayya Ta 10

A wani labarin na daban kuma Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana sabbin shugabannin da zasu jagoranci majaliaa ta 10.

Abbas ya ayyana Farfesa Julius Ihonvbere daga jihar Edo kuma mamban APC a matsayin sabon shugaban masu rinjaye da kuma Usman Kumo daga Gombe a matsayin mai ladabtarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262