Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Villa

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Villa

  • Tsohon ministan ilimi da ya sauka, Adamu Adamu, ya ziyarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
  • Har yanzu babu cikakken bayani game da ziyarar Adamu, wanda ya shafe shekaru 8 kan kujerar Ministan ilimi a gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Sai dai 'yan Najeriya sun maida martani inda suka nuna fatan ganin shugaba Tinubu ya kama tsohon ministan domin bincikarsa

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na ganawa yanzu haka da tsohon ministan ilimi da ya gabata, Adamu Adamu, a fadar shugaban ƙasa Aso Rock, Abuja.

Mista Adamu ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 1:30 na rana yau Talata, 4 ga watan Yuli, 2023 kuma daga isarsa ya shiga taron sirri da Bola Tinubu.

Shugaba Tinubu da Adamu Adamu.
Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Villa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Adamu Adamu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa ba bu wani cikakken bayani kan maƙasudin wannan ganawa ko kuma muhimman batutun da zasu tattauna a taron.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Kammala Bincike Kan Mmesoma Ejikeme, Dalibar Da Ta Yi Karyar Cin Maki 362

Sai dai duk da ba'a bayyana ajendojin wannan zama ba amma taron ya zo ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin Ministocin da shugaban ƙasan ke shirin tura wa majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Najeriya sun maida martani kan ziyarar da Adamu ya kai wa Tinubu

Ga dukkan alamu wannan ganawa da Tinubu ya yi da tsohon ministan ilimi a gwamnatin Buhari ba ta yi wa 'yan Najeriya daɗi ba.

Wani mai amfani da shafin tuwita, #MisterMax @lummax12 ya ce ba bu dalilin da shugaban ƙasa zai tsaya ɓata lokacinsa da Adamu matuƙar da sanya wa zai yi a kama shi ba.

"Dalili ɗaya da zai sa na ji daɗin karban bakuncin da shugaban ƙasa ya yi masa shi ne na ji labarin an damƙe shi daga nan zuwa ƙarfe 8:00 na dare. Bamu son maimaita faɗuwa dan Allah."

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Fadi Yayin Rangadi? Gaskiya Ta Bayyana

Wani ɗan Najeriya na daban, @Collins_Paul_cp ya ce:

"Ina fatan wannan zaman na shirin cafke shi ne. Ministan ilimin da ya bar ilimi cikin ƙaƙanikayi."

A B D U L @abdul_husayn kuma ya yi kira ga shugaban ƙasa ya sa a garkame tsohon ministan a gidan gyaran hali.

"Da kyau, a tura shi magarƙama."

Shugaban APC, Mambobin NWC Suna Ganawa da Gwamnoni a Abuja

A wani labarin na daban kuma Mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) sun shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC (PGF) a birnin tarayya Abuja.

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, mataimakansa na kudu da arewa da sauran jiga-jigai sun halarci zaman yau Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262