Tajuddeen Abbas Ya Nesanta Kansa Da Munanan Kalaman Da Hadiminsa Ya Yi A Kan Buhari

Tajuddeen Abbas Ya Nesanta Kansa Da Munanan Kalaman Da Hadiminsa Ya Yi A Kan Buhari

  • Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya nesanta kansa daga kalaman da daya daga cikin hadimansa ya yi akan tsohon shugaban kasa
  • Godfrey Gaiya, wanda hadimi ne ga kakakin majalisar, ya yi wasu kalamai na rashin da'a ga Muhammadu Buhari
  • Da yake mayar da martani, kakakin Majalisar Wakilan ya ce kalaman da Gaiya ya yi a hira da aka yi da shi nasa ne na kashin kansa

Abuja - Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya nesanta kansa daga wata hira da daya daga cikin hadimansa Godfrey Gaiya ya yi, wacce ake ganin cin mutunci da cin fuska ce ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata sanarwa da ta fito ta hannun mai ba kakakin majalisar shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Kirshi, ta ce kalaman Mista Gaiya kan Buhari ra'ayinsa ne na kashin kansa ba na Tajuddeen ba, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda Amintaccen Minista Ya Yaudari Buhari Ana Saura Awanni Tinubu Ya Karbi Mulki

Kakakin Majalisar Wakilai ya barranta da kalaman hadiminsa
Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas ya barranta da kalaman da hadiminsa ya yi a kan Buhari. Hoto: Bashir Ahmad / Daily Nigerian
Asali: Facebook

Kalaman da hadimin Tajuddeen Abbas ya yi a kan Buhari

Gaiya a hirar da ya yi da wata jarida a makon da ya gabata, ya soki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce ya gaza yin abubuwan da ‘yan Najeriya ke zato daga gareshi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gaiya ya kuma ce an samu karuwar cin hanci da rashawa, nuna son kai, da kuma jefa 'yan kasa cikin wahala a gwamnatin Buharin, Tribune ta rahoto.

Da aka tambayi Mista Gaiya a cikin hirar ko me zai gaya wa Buhari idan suka hadu ido da ido? sai ya amsa da cewa:

“Zan fada masa a fili cewa ya gaza, zan ce masa Buhari ka gaza."
"Ya yaudari ’yan Najeriya da cewa shi na kirki ne, alhalin shi ma a boye cike yake da rashawa ta Allah tsine."

Kara karanta wannan

“Buhari Yana Landan Don Jinya Kamar Yadda Ya Saba”, Rafsanjani Ya Yi Zargi

“Mun gani kuma za mu ga adadin mutanen da suka zama hamshakan masu kudi a gwamnatin Buhari."
“Idan ba ka yaki cin hanci da rashawa ba, ko ka ki juyawa abun ki baya, ka bar shi ya ci gaba da wakana, a lokacin da kake da cikakkiyar damar dakatar da shi, za a ce kawai ka gaza."
“Don haka Buhari ya gaza ta fannoni da dama. Mu ne kasar da ta fi kowacce kasa cin bashi a Afirka a karkashin mulkin Buhari na tsawon shekaru takwas.”

Martanin Abbas Tajuddeen kan kalaman da hadimin nasa ya yi a kan Buhari

Wadannan kalamai ne suka sa kakakin majalisar ya dage cewa mai taimakamasa ya yi hirar ne ba tare da amincewar sa ba.

Sanarwar da kakakin ya fitar ta na cewa:

“Sako ya iso zuwa ga Kakakin Majalisar Wakilai, Onarabul Tajudeen Abbas (PhD), cewa daya daga cikin mataimakansa ya yi hira da wata jarida, inda ya yi wasu kalamai da ba su dace ba.”

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Bar Mahaifarsa Ta Daura, Cikakken Bayani Ya Bayyana

“Yana so a sani cewa, wannan mai taimaka masa, mai suna Onarabul Godfrey Gaiya, ba shi da sahhalewar kakakin majalisar don yin irin wannan hirar. A don haka kalaman da Godfrey Gaiya ya yi nasa ne ba na kakakin majalisa Tajudeen Abbas ba."
“Domin kaucewa shakku, Kakakin Majalisa, Onarabul Tajudeen Abbas (PhD), yana da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama'a, wanda ke aiki a matsayin mai magana da yawunsa. Dukkanin wasu bayanan da shugaban majalisar ya fitar a hukumance, suna fitowa ne daga bakinsa."

Tajuddeen Abbas na mutunta Buhari da El-Rufai

Sanarwar ta kuma bayyana cewa yana da kyau jama'a su san cewa kakakin majalisar na mutunta Buhari, kuma shi ma Buharin na mutuntasa.

Haka nan Tajuddeen yana mutunta tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai kamar yadda shi ma yake mutuntasa.

A saboda haka sanarwar ta ce kakakin majalisar ba zai fadi ko kuma ya yi wani abu ba da zai shafi kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan

‘Na Shekara 4 Da Makanta’: Labarin Makaho Da Ke Amfani Da Wayar ‘IPhone’ Ya Girgiza Intanet

This Day ta wallafa cewa, Tajuddeen da mataimakinsa Benjamin Kalu, a wata sanarwa da Krishi ya fitar, sun ziyarci Abdullahi Adamu a lokacin shagalin Sallah, inda suka ce ya jagoranci jam’iyyar zuwa ga nasara a babban zaben 2023, tare da tabbatar da samun shugabancin majalisa ta 10 kamar yadda yake a tsarin shiyya-shiyya na APC.

Da yake jawabi, Adamu ya godewa shugaban majalisar, mataimakin shugaban majalisar da sauran ‘yan jam’iyyar APC bisa yadda suka yi biyayya ga jam’iyyar musamman a lokacin kaddamar da majalisar ta goma.

Shugaban APC Abdullahi Adamu ya yi kira ga shugabannin majalisun tarayya su taimaki Tinubu

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto inda shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya yi kira ga shugabannin Majalisun Tarayya da su samar da tsare-tsaren da za su taimaki gwamnatin Tinubu.

Adamu ya bayyana hakan ne a yayn wata ziyara da shugaban Majalisar Wakilai, Godswill Akpabio ya kai masa a gidansa da ke Keffi jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng