“Bai Da Alaka Da Siyasa”: Gwamna Otti Ya Magantu Kan Rashin Ganin Hotunan Tinubu a Ofishoshin Gidan Gwamnati
- Hotunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai ratsa dukkanin ofishoshi a gidan gwamnatin jihar Abia
- Mai bayar da shawara ta musamman ga gwamna Alex Otti kan harkokin labarai, Ferdinand Ekeoma, ya ce lamarin bai da nasaba da siyasa
- Ekeoma ya ce hatta hotunan Gwamna Otti basa cikin dukka ofishoshi a gwamnatin, yana mai cewa sun ba da umurnin karo hotunan shugaban kasa Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Abia - Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya yi bayanin dalilin da yasa babu hotunan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a dukka ofishoshin da ke gidan gwamnati a Umuahia.
Kamar yadda jaridar PM News ta rahoto, Otti ta hannun hadiminsa, Ferdinand Ekeoma, ya bayyana cewa sabuwar gwamnati ce ta shigo kuma gwamnatin jihar ta sanya hotunan Tinubu a cikin wasu ofishoshin sannan sun yi umurnin a karo wasu hotunan.
Hotunan Gwamna Otti ma basu ratsa dukka ofishohin gidan gwamnatin Abia ba
Ekeoma ya ce akwai hotunan shugaban kasar a cikin wasu ofishoshi, yana mai cewa irin haka ne a bangaren Gwamna Otti.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan ya yi watsi da ikirarin cewa an ki sanya hotunan ne saboda gwamnatinsa bata dauki Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya ba.
Daily Trust ta rahoto Ekeoma yana cewa:
"Ba mu da hotunan gwamnan a yawancin ofishoshi saboda wannan sabuwar gwamnati ce. Mun sanya wasu hotuna sannan mun yi umurnin kawo karin wasu.
"Ranar da gwamnan ya hadu da sakatarorin din-din hotunan tsohon Gwamna Ikpeazu ne a babban dakin taron.
"Laifi ne a ce ba za a dauki mutumin da aka rantsar bisa ka'ida a matsayin shugaban kasa ba. Hankali ba zai dauka ba kuma bama tunani ta wannan hanyar."
An bukaci Tinubu ya ajiye Wike sannan ya nada wani shahararren da siyasar Ribas minista
A wani labari na daban, gamayyar kungiyar dattawan jihar Ribas a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli, sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya nada Sanata Magbys Abe a matsayin daya daga cikin ministocinsa.
An tattaro cewa wannan bukatar na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jagoran kungiyar, Sunnie Chukumele, da sakataren kungiyar, Josiah Onoriode.
A cewarsu, za su yi farin ciki da ganin shugaban kasa Tinubu ya zabi Sanata Abe cikin majalisar zartarwa ta tarayya wanda ke gab da kafawa.
Asali: Legit.ng