An Bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Nada Magnus Abe a Matsayin Minista
- Wata kungiya ta shugabannin jihar Ribas, ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya duba yiwuwar nada Sanata Magnus Abe a matsayin minista
- Shugabannin sun yi bayanin cewa sun lura da yadda kwatsam shugaban kasa Tinubu ya yi watsi da Sanata Abe
- Kungiyar ta ce Abe ne ainahin mai biyayya ga Tinubu a jihar Ribas, wanda shi kadai ne ya samar da tsanin siyasar da suka marawa shugaban kasar baya a zaben 2023
Rivers - Gamayyar kungiyar shugabannin jihar Ribas a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli, sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya nada Sanata Magbys Abe a matsayin daya daga cikin ministocinsa.
Kamar yadda jaridar PM News ta rahoto, wannan bukatar na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jagoran kungiyar, Sunnie Chukumele, da sakataren kungiyar, Josiah Onoriode.
Ka ba Magnus Abe mukamin minista, kungiya ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu
Kungiyar dattawan na Ribas sun bayyana cewa za su yi farin ciki da ganin shugaban kasa Tinubu ya zabi Sanata Abe cikin majalisar zartarwa ta tarayya wanda ke gab da kafawa, rahoton The Punch.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwar ta ce:
"Mun lura cewa an mayar da Sanata Magnus Ngei Abe saniyar ware ko an ture shi kefe a shirye-shiryen al'amuran siyasa a fadar shugaban kasa.
"Mun yarda cewa nada Sanata Abe, wanda takardunsa suke firgitar da yan maza, a majalisar shugaban kasa Tinubu zai karfafa ainahin wadanda suka yarda da shugaban kasar da mabiyansa na gaskiya a jihar."
Buhari bai nemi Tinubu ya dakatar da binciken Emefiele da tsoffin jami'an gwamnatinsa ba, Garba Shehu
A wani labari na daban, tsohon kakakin tsohon shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya karyata rahotannin da ke yawo cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da binciken tsoffin yan majalisarsa.
Shehu ya jaddada cewar tsohon shugaban kasar na nan a kan bakarsa na kin tsoma baki a al'amauran da suka shafi sabuwar gwamnati mai ci don haka labarin cewa ya nemi a dakatar da bincike ba gaskiya bane bai da tushe balle makama.
A cewarsa, hasalima tsohon uban gidan nasa ya bar mahaifarsa ta Daura zuwa wani waje mai dan nisa domin ya samu isasshen hutun da yake bukata.
Asali: Legit.ng