Shugaba Bola Tinubu Ya Dira Jihar Ogun, Ya Kai Ziyara Fadar Sarki Awujale
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa jihar Ogun a wata ziyara ta musamnan da ya kai karon farko tun bayan ɗarewa kan madafun iko
- Tinubu ya ziyarci fadar mai martaba sarkin ƙasar Ijebu, Oba Sikiru Adetona domin gode masa bisa dumbin goyon bayan da ya samu daga sarakuna
- Da yake jawabi a fadar basaraken, shugaba Tinubu ya ce ya kira ruhin yanci a jihar Ogun lokacin da tawagarsa ta je kamfe gabanin zaɓe
Ogun State - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya dira jihar Ogun domin kai ziyara ta farko tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya na 16.
Jaridar Punch ta tattaro cewa yanzu haka shugaban kasar ya ziyarci fadar Awujale, babban Sarkin kasar Ijebu, Oba Sikiru Adetona.
Waɗanda suka halarci wurin tare da shugaban ƙasa sun haɗa da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, tsohon gwamna, Gbenga Daniel, mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Rabaɗu da sauran jiga-jigai.
Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Zai Gana da Wasu Manyan Sarakuna a Fitacciyar Jihar APC, Bayanai Sun Fito
Ina miƙa godiya mara adadi ga sarakuna da sauran al'umma - Tinubu
Da yake gode wa mai masaukin baƙi, shugaba Tinubu ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na kawo ziyara gidanmu kuma kuna bi na basussuka da yawa, ban san da wake kalamai zan gode muku ba saboda yadda kuka ɗauke ni, da yadda kuka yi ɗawainiya da ni, na gide muku sosai."
"Saƙo gare ku baki ɗaya, ina kara miƙa godiya gare ku bisa yadda kuka taimaka mun, kuka tsaya wa ƙasar nan. Kun nuna jajircewa da sadaukarwa kuka kaɗa kuri'unku a lokaci mai tsananin wahala."
"Ƙiri-kiri aka riƙe muku kudadenku duk da tsarin sauya fasalin kuɗin da suka zo da shi bai tasira a kanmu ba duk da an shiga yanayin wahala. Nan Ogun na zo na kira ruhin yanci."
Idan baku manta da yayin kamfen shugaban ƙasa na APC a jihar Ogun, Tinubu ya yi ikirarin karancin mai da sauya fasalin kudi duk manaƙisa ce ta ganin bayansa a zabenn 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya
Gwamna Radda Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi a Jihar Katsina
A wani labarin na daban kuma Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya yi sabbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa.
Naɗe-naɗen sun fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin jiha, Ahmed Musa Dangiwa, ta hannun sakataren watsa labaran gwamna.
Asali: Legit.ng