Uba Sani Ya Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Kwangilolin Da El-Rufai Ya bayar
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani zai binciki kwangilolin da aka bayar a lokacin gwamnatin El-Rufai
- Gwamnan dai ya kaddamar da wani kwamiti ne mai dauke da mutane takwas da za su gudanar da ayyukan binciken
- Kwamitin zai bincika duk wasu ayyuka da aka fara da ma wadanda ba a fara gudanarwa ba a fadin jihar
Kaduna - Gwamnantin jihar Kaduna, karkashin jagorancin Sanata Uba Sani, ta sanar da kafa wani kwamiti da zai tantance matsayin duk wasu ayyuka da ke gudana a fadin jihar.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Mohammed Shehu ya fitarwa manema labarai ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Ayyukan da kwamitin na Uba Sani zai bincika
A cewar sanarwar, kwamitin da aka kafa zai duba duk wasu ayyuka da ba a riga da an fara ba, wadanda gwamnatin tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ta bayar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakan ya yi daidai da yunkurin gwamnatin na ganin an gaggauta kammala duk wasu ayyukan da suka tasa a gaba.
Daga cikin ayyukan da wannan kwamiti zai gudanar akwai:
1. Gane matsayin duka ayyukan da ake gudanarwa yanzu a fadin jihar.
2. Samun cikakkun bayanai game da yarjejeniyar da aka kulla wajen ba da kwangilar.
3. Nemo tsare-tsare na kudade da alkawurran da duka bangarorin suka kulla.
4. Gano lokacin da ya kamata a kammala kowane aiki.
5. Zuwa da shawarwari na musamman kan ayyukan da ake gudanarwa.
Gwamna Uba Sani ya bai wa kwamitin makonni hudu kacal daga randa aka kaddamar da shi domin gabatar da rahotonsa.
Sunayen mambobin kwamitin bincike da sanya idanu da Uba Sani ya kafa
Sunayen mutanen wannan kwamiti da Uba Sani ya kafa kamar yadda Premium Times ta wallafa sune:
Sabiu Sani, mai ba da shawara na musamman kan harkokin zuba jari da haɓaka kasuwanci – a matsayin shugaban kwamitin
Abdullahi B. Ahmed, mai bayar da shawara na musamman kan sanya idanu kan ayyukan, aiwatarwa da bayar da sakamako - wanda mamba ne a kwamitin
Mustapha Musa, mai bayar da shawara na musamman, kan harkokin shari'a - shi ma mamba ne a kwamitin
Fabian Okoye, mai bayar da shawara na musamman kan bincike, tattara bayanai da dabarbaru na aiki - shi ma mamba ne a kwamitin
Ibrahim T. Muhammad, mai bayar da shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki – shi ma mamba ne a kwamitin
Atiku Sankey, mai bayar da shawara na musamman kan zaman lafiya da warware rikici - shi ma mamba ne a kwamitin
Larai Ishaku – mamba a kwamitin
Shuaibu Kabir Bello, babban mataimaki na musamman a bangaren ICT – wanda shi ne sakataren kwamitin
Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Bayyana Irin Matakin Da Za Ta Dauka Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)
Uba Sani shi ne ya gaji tsohon gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris na 2023 da ya gabata.
Sai dai kuma, dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar ta Kaduna, Isah Ashiru Kudan na kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu.
Kiristoci a Kaduna sun taya Musulmai share masallacin Idi
Wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa, Kiristoci a jihar Kaduna, sun taya Musulmai sare ciyayi a masallacin da suke gudanar da sallar Idi.
Hakan ya faru ne a daidai lokacin da Musulmi ke shirye-shiryen gudanar da bukukuwan babbar sallah.
Asali: Legit.ng