Gwamna Radda Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi a Jihar Katsina

Gwamna Radda Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi a Jihar Katsina

  • Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗda ya naɗa shugabannin hukumomin gwamnati 9 a jihar Katsina
  • Naɗe-naɗen sun fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin jiha, Ahmed Musa Dangiwa, ta hannun sakataren watsa labaran gwamna
  • Radɗa ya naɗa shugaban hukumar tallafin karatun ɗalibai, hukumar ilimin bai ɗaya da sauran wasu hukumomi 7

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Katsina State - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa,ya naɗa sabbin shugabannin wasu hukumomin gwamnati a jihar Katsinan dikko.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa sakataren watsa labarai na gwamnan Katsina, Ibrahim Kuala Mohammed, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗda.
Gwamna Radda Ya Nada Sabbin Shugabannin Hukumomi a Jihar Katsina Hoto: Dr Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Sanarwan ta yi bayanin cewa naɗe-naɗen sun fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin Katsina (SSG), Ahmed Musa Dangiwa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Jerin mutanen da Malam Raɗda ya naɗa da hukumomin da zasu jagoranta

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Manyan Naɗe-Naɗe 2 a Karon Farko

Sanarwan ta jero mutanen da Malam Dikko Raɗɗa ya nada da kuma hukumomin da zasu jagoranta, ga su kamar haka:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Alhaji Kabir Usman Amoga - Daraktan hukumar tsaftace mahalli ta jihar Katsina.

2. Hajia Binta Dangani - Shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta Katsina.

3. Injiniya Tukur Tinglin - Babban Darektan hukumar samar da ruwa.

4. Honorabul Abubakar Sulaiman Abukur - Daraktan hukumar samar da ruwa a karkara da tsaftace muhalli.

5. Dakta Nuhu Bala Kankia - Shugaban hukumar shawo kan cuta mai karya garkuwar jiki ta Katsina.

6. Dakta Aliyu Rabi'u Kurfi - Shugaban hukumar tarihi da al'adu ta jihar Katsina.

7. Farfesa Kabir Ibrahim Matazu - Shugaban hukumar kimiyya da fasaha.

8. Dakta Aminu Salisu Tsauri - Shugaban hukumar ba da tallafin karatu ta jiha.

9. Alhaji Kabir Magaji - Shugaban hukumar kula da ilimin bai ɗaya (SUBEB) ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Dakatar da Ciyamomin Kananan Hukumomi 23, PDP Ta Maida Martani Mai Zafi

Gwamna Raɗɗa na jam'iyyar APC ya karɓi mulki daga tsohon gwamna, Aminu Bello Masari, bayan lashe zaɓen 18 ga watan Maris, 2023.

Ganduje Ya Koka Kan Matakin Abba Gida Gida Na Dakatar da Albashin Ma'aikata 10,000

A wani labarin na daban kuma Tsohon Gwamna Ganduje ya koka kan matakin da Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na dakatar da albashin ma'aikata sama da 10,000 a Kano.

Ganduje ya ce wannan wani yunkuri ne da ke nuna manufar sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusuf na korar ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262