Ganduje Ya Koka Kan Matakin Abba Gida Gida Na Dakatar da Albashin Ma'aikata 10,000
- Tsohon gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nuna damuwarsa da matakin dakatar da albashin ma'aikata sama da 10,000 a Kano
- Ganduje ya ce wannan wani yunkuri ne da ke nuna mafufar sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusuf na korar ma'aikata
- Ya kuma ƙara kokawa kan soke karin girman da gwamnatinsa ta yi wa wasu malaman makaranta a faɗin Kano
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano state - Tsohon gwamnan jihar Kano da ya gabata, Abdullahi Ganduje, ya koka kan matakin dakatar da albashin ma'aikatan da ya ɗauka aiki sama da 10,000.
Vanguard ta tattaro cewa Ganduje ya nuna rashin jin daɗinsa bisa matakin da gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauka kan ma'aikatan a daidai lokacin da ake shirye-shiryen shagalin Sallah.
Hakan na kunshe ne a sakon Barka da Sallah da Ganduje ya fitar ta hannun tsohon kwamishinan yaɗa labarai, Muhammad Garba, ranar Laraba, 28 ga watan Yuni.
Abinda hana ma'aikatan albashi ya jawo - Ganduje
Dakta Ganduje ya ƙara da cewa dakatar da albashin ya jefa tsoro a zuƙatan ma'aikatan jihar Kano domin alama ce ta yuwuwar tankaɗe da rairaya a lokacin da kowa ke fama da rayuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa, ya ce:
"A daidai lokacin da muke shagalin murnar sallar layya, ita kuma gwamnatin NNPP ta dakatar da albashin ma'aikata sama da 10,000, waɗanda tsohuwar gwamnati ta ɗauka aiki."
"Dakatar da albashin, wanda ya shafi ma'aikata musamman malaman makaranta ya sanya tsoro a zuƙatan bangaren ma'aikata baki ɗaya domin alama ce ta yuwuwar korar wasu."
"Ban ji daɗin yadda aka soke ƙarin girman da wasu malaman makaranta suka samu ba da kuma biyansu albashi a matakin da suka baro. Waɗanda matakan na sabuwar gwamnati ba su zo mana da mamaki ba."
Menene manufar gwamnatin Kano?
Tsohon gwamnan ya kara da cewa bai yi mamakin waɗan nan matakin masu tsauri da sabuwar gwamnati ke ɗauka ba domin sun fara haka ne domin rage wa ma'aikata albashi.
A ruwayar Leadership, Ganduje ya ci gaba da cewa:
"Wannan matakin alamu ne da ke nuna shirinsu na korar Malamai su maye gurbinsu da mambobin jam'iyyarsu."
Shugaba Tinubu Zai Gana da Sarakunan Jihar Ogun Yau Alhamis
A wani rahoton na daban Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya kai ziyara Abeokuta da Ijebu-Ode a jihar Ogun ranar Alhamis (yau) 29 ga watan Yuni, 2023.
Hadimin gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, Babatunde Olaotan, ne ya bayyana haka ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, 2023.
Asali: Legit.ng