An Zargi Tsohon Ministan Buhari, Timipre Sylva Da Yin Barazana Ga Rayuwar Mutumin Atiku Timi Frank

An Zargi Tsohon Ministan Buhari, Timipre Sylva Da Yin Barazana Ga Rayuwar Mutumin Atiku Timi Frank

  • Rikicin da ya barke tsakanin Timipre Sylva, tsohon minista a lokacin Buhari, da Timi Frank, tsohon kakakin jam’iyyar APC ya yi kamari
  • A ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, Timi Frank ya kai kokensa zuwa ga babban sufeto janar na ‘yan sanda, Olukayode Egbetotkun, bisa zargin barazana ga rayuwarsa da ya ce ana yi
  • Frank, a cikin kokensa ga ‘yan sanda, ya bayyana tsohon karamin ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva, a matsayin babban wanda yake zargi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Birnin Tarayya, Abuja - Tsohon mataimakin kakakin jam’iyyar APC, kwamared Timi Frank wanda a yanzu mutumin Atiku ne, ya zargi tsohon karamin ministan albarkatun man fetur na kasa, Cif Timipre Sylva, da yin barazana ga rayuwarsa.

Kwamared Frank ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Gwamna Ya Gaza Sallatar Idi Sakamakon Wani Sanata Da Ya Tsare Masa Wuri

Frank ya ce ya kai kararsa zuwa ga babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, Olukayode Egbetotkun domin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace.

An zargi minista a lokacin Buhari da yin barazanar ran wani
An kai karar Timipre Sylva bisa zargin barazana da rayuwa. Hoto: Tim Frank, Timipre Sylva
Asali: Facebook

Frank ya ce duk abinda ya same shi, a tuhumi Sylva

A cikin bayanin sa da Legit.ng ta samu, Frank, wanda kuma dan rajin kare hakkin dan adam ne, ya bayyana cewa idan wani abu ya same shi ya zama dole a tuhumi tsohon gwamnan jihar Bayelsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin koken mai dauke da kwanan wata Laraba, 28 ga watan Yuni, 2023, mai taken “ci gaba da barazana ga rayuwar Kwamared Timi Frank”, tsohon mataimakin kakakin jam’iyyar APC ya ce:

“Kara a kan Cif Timipre Sylva kan aikata laifukan da suka shafi satar suna, sojan gona, amfani da takardun karatu na jabu, da bayar da shaidar karya da ta sabawa sashe na 486 na kundin laifuffuka, CAP C38 Dokokin Tarayyar Najeriya 2004 tare da sashe na 366 , 364 da 158 (2) na Dokar Penal Code, CAP 532 Dokokin Tarayyar Najeriya (Abuja) 1990."

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

“Batun da ke sama da kuma koken mu mai kwanan wata 22 ga Mayu, 2023 wanda aka baka a tsohon ofishinku na Hukumar Leken Asiri da Binciken Manyan Laifuka (FCIID), Rundunar ‘Yan sandan Najeriya, Area 10, Garki, Abuja a ranar 26 ga Mayu, 2023 yana nufin:"
"Mun rubuto sako ne don bayar da rahoto cewa yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Cif Timipre Sylva ya koma yin barazana ga rayuwar abokin aikinmu, Kwamared Timi Frank, saboda jajircewarsa wajen yin fallasa game da abubuwan da ke ƙunshe a cikin takaddun karatunsa."

Timi Frank ya kara kai koke a kan Sylva

Kamar yadda takardar da lauyansa, Edward Omaga ya sanya wa hannu, ya yi nuni da cewa, a tarihin Nijeriya a matsayin kasar da ake gudanar da dimokuradiyya bai taba zama laifi ba a ce dan kasa mai kishin kasa irin Timi Frank ya fallasa cin hanci da rashawa ba ta masu rike da mukaman gwamnati ko wadanda suka yi ritaya.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi

Takardar koken kamar yadda The Guardian ta samu tana cewa:

"Muna fatan za ka dauki matakin gaggawa da zai iya kare rayuwar abokin huldarmu kamar yadda yake a jadawalin ayyukanka na doka a karkashin sashe na 4 na dokar 'yan sanda, 2020."
"Muna da yakinin cewa a matsayinka na mai hazaka da rikon amana, za ka yi duk mai yiwuwa don tabbatarwa masu sanya idanu na cikin gida da na kasashen waje, cewa aikata laifuka ba za su samu gindin zama ba a Najeriya."

An caccaki dan takarar shugabancin kasa saboda hasashensa kan shari'ar Atiku

Legit.ng a baya ta kawo muku labari kan caccakar da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar SDP ya sha, saboda hasashen da ya yi a kan shari'ar Atiku da Obi da suke da Tinubu.

Masu amfani da kafar sada zumunta sun masa martani mai zafi sabili da nunawa da ya yi kamar cewa suna bata lokacinsu ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng