Buhari: Shugabancin Najeriya Na Daya Daga Cikin Kalubale Mafi Tsanani A Rayuwa
- Tsohon shugaban Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa shugabanci a Najeriya cike yake da kalubale mai yawa
- Buharin ya bayyana hakan ne a cikin wani sako na barka da sallar Eid-el-Kabir da ya aikewa 'yan Najeriya
- Hakan na zuwa ne a kasa da sa'o'i 24 da Buhari ya yi jawabi kan abinda ya hana shi cire tallafin man fetur
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana shugabancin Najeriya a matsayin daya daga cikin kalubale mafi tsanani a rayuwa.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na taya murnar babbar sallah, wato Eid-el-Kabir ga ‘yan Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Buhari ya mika ragamar mulki ga shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023, wanda daga nan ne ya koma gefe yana rayuwarsa shi kadai.
Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya su ba Tinubu goyon baya
A cikin sanarwar, wacce Mallam Garba Shehu, tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasar ya fitar a ranar Talata, Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su goyawa magajinsa baya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar sanarwar:
“Jagoranci kasa kamar Najeriya na daya daga cikin kalubale mafi wahala a rayuwa kuma ya bukaci ‘yan Najeriya da su bai wa gwamnatin Tinubu cikakken goyon baya don samun nasara, saboda shugabanci aiki ne mai cike da kalubale da ke bukatar sadaukarwa da goyon bayan ‘yan kasa.”
Buhari ya bayyana dalilin da ya hana ya cire tallafin man fetur
Buhari ya fadi hakan ne cikin abinda bai wuce sa’o’i 24 da ya yi ikirarin cewa, Tinubu zai fadi zabe in a ce ya cire tallafin man fetur.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin din da ta gabata, Buhari ya kare matakin da ya dauka na kin cire tallafin man fetur a lokacin da yake kan mulki.
Ya bayyan cewa bai cire tallafin ba ne domin gudun kada jam’iyyar APC ta fadi zaben 25 ga watan Fabrairu da ya gabata.
Shehu ya ce akwai tallafi da dama da gwamnatin Buhari ta gada a shekarar 2015, amma duka ya ciresu kafin ya sauka mulki.
Ya ce akwai tallafe-tallafe irin na man dizal, na man jirgin sama, kalanzir, gas din girki da sauransu, wadanda Buhari ya gada amma ya cire su kafin ya sauka mulki.
Sai dai dama tun a lokacin da yake kan madafun iko, tsohon shugaban kasar, ya taba bayyana cewa ba za a iya ci gaba da biyan kudaden tallafin man fetur ba daga 2023.
GwamnatinTinubu za ta samar da ayyukan yi miliyan 1 ga 'yan Najeriya
Legit.ng ta kawo muku rahoto a baya da yake cewa, gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, za ta samar da ayyukan yi akalla miliyan daya ga matsan Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da wakilan shugaban Kasar Koriya ta Kudu a Abuja.
Asali: Legit.ng