Babban Jigo a APC Ya Bayyana Dalilin Da Yakamata Wike Ya Dawo APC Ya Jagoranceta a Jihar Rivers

Babban Jigo a APC Ya Bayyana Dalilin Da Yakamata Wike Ya Dawo APC Ya Jagoranceta a Jihar Rivers

  • Nyesom Ezenwo Wike ya samu goyon bayan wani jigo a jam'iyyar APC domin ya marawa jam'iyyar baya a jihar Rivers
  • Iyke Ejie ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Rivers yana da ikon komawa jam'iyyar APC sannan ya zama jagoranta a jihar
  • Jigon na jam'iyyar APC ya bayyana cewa ba don goyon bayan Wike ba, da Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya sha kashi a jihar Rivers

FCT, Abuja - Wani babban jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Iyke Ejie, ya nuna goyon bayansa kan batun komawar tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike zuwa jam'iyyar mai mulki.

Ejie wanda mamba ne a kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu-Shettima a jihar Rivers, ya bayyana cewa da ba don Wike ba, da jam'iyyar APC ba ta yi nasara ba jihar, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Jigo a Jam'iyyar PDP Ya Shirya Kwance Wa Jam'iyyar Zani a Kasuwa a Gaban Kotu

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni, ya bayyana cewa yakamata Wike ya dawo APC domin ya jagoranceta a jihar Rivers.

Jigon APC ya goyi bayan Wike ya dawo APC
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Rivers yana da ƴancin shiga kowace jam'iyya sannan ya nemi shugabanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ejie ya bayyana cewa:

"Da ba don goyon bayan Wike ba, APC ba za ta ci zaɓe ba a jihar. Lokacin da abubuwa suka taɓarɓare, gwamnan ya nuna goyon bayansa ga Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya goge sosai a siyasa kuma aka yi na'am da shi."
"Kada a manta, ya jagoranci gwamnonin G-5 wanda suka tsaya bayan gaskiya, adalci da daidaito suka haƙiƙance sai shugaban ƙasa ya fito daga yankin Kudu. Sannan ya tabbatar Tinubu ya yi nasara wanda shi kansa shugaban ƙasar sai da ya yaba lokacin da ya zo ziyarar godiya a jihar Rivers."

Kara karanta wannan

Fitaccen Mamban APC Ya Magantu Kan Sauya Shekar Tsohon Gwamnan PDP Zuwa APC

Wike ya taka rawa wajen ganin Tinubu ya zama shugaban ƙasa

Jigon na jam'iyyar APC ya ƙara da cewa Wike ya tabbatar cewa yankin Kudu ya samu shugaban ƙasa inda ya jajirce wajen ganin nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

"Bari na faɗa ba tare da wata tantama ba Wike ya tabbatar da nasarar Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya fito daga yankkn Kudu a bisa kuɗirinsa da na gwamnonin G-5 cewa mulki ya koma Kudu." A cewarsa
"Maganar gaskiyar ita ce Cif Tony Okocha shi ne shugaban jam'iyyar APC a jihar Rivers sannan ina sake nanata kiran Wike ya dawo APC a jihar Rivers ya jagorance mu saboda mutum ne mai hangen nesa wanda za a iya yarda da shi. Yana da ƴancin shiga duk jam'iyyar da ta kwanta masa a rai."

Hadimin Wike Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Atiku Ya Fadi Zabe

A wani labarin na daban kuma, hadimin tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sanya Atiku Abubakar ya sha kashi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kara karanta wannan

Manyan Jiga-Jigan PDP da Dubannin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC Ana Tunkarar Zaɓe a Jihar Arewa

Marshal Obuzor ya bayyana cewa girman kan Atiku a siyasa shine maƙusudin dalilin da ya sanya bai kai labari ba a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng