Yadda Obi da Ayu Suka Taimaka Atiku Ya Faɗi Zaben Shugaban Kasa 2023, Sanata

Yadda Obi da Ayu Suka Taimaka Atiku Ya Faɗi Zaben Shugaban Kasa 2023, Sanata

  • Tsohon Sanata ya bayyana cewa Ayu da Peter Obi ne suka ja Atiku Abubakar ya sha kashi a babban zaben 2023
  • Matthew Urhoghide, ya ce rikicin Ayu da gwamnonin G5, da kuma fitar Obi zuwa LP ne asalin inda matsalar ta samo asali
  • Bola Tinubu na jam'iyyar APC ne ga samu nasarar lashe zaɓen shugaban kasa wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023

Tsohon sanatan Enugu ta kudu, Matthew Urhoghide, ya bayyana mutum biyu da yake kallo da laifin rashin masarar ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar a zaɓen 2023.

Ya ce rigimar shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, da tawagar gwamnonin G5 da kuma ficewar Peter Obi zuwa jam'iyyar LP ne manyan abu 2 da suka haddasa rashin nasarar Atiku.

Atiku Abubakar, Nyesom Wike da Iyorchia Ayu.
Yadda Obi da Ayu Suka Taimaka Atiku Ya Faɗi Zaben Shugaban Kasa 2023, Sanata Hoto: Atiku Abubakar, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Urhoghide, wanda ba da jimawan nan ba ya fice daga PDP, ya yi wannan furucin ne a cikin shirin Politics Today na ƙafar watsa labaran Channels tv ranar Litinin.

Kara karanta wannan

NSA: Sabon Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaron Kasa Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

"Wannan zaɓen na Atiku ne domin ko APC ta san shi ne ya kamata ya samu nasara. Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kansa ya san rabuwar kan mu ta ja mana faɗuwa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan ne abinda tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ke nufi lokacin da ya zo nan," inji shi.

Da jam'iyyar PDP ta dunƙule ba haka sakamakon zai kasance ba - Urhoghide

A rahoton jaridar Punch, Sanatan ya ƙara da cewa sakamakon zai iya sauya wa idan da tun farko jam'iyyar PDP ta haɗa kan 'ya'yanta.

"Da tun farko an rarrashi Peter Obi ya zauna a PDP, zamu ruɓanya kuri'un da muka samu a zaɓen 2019 saboda kuri'un da ya samu a zaben da ya gabata zasu dawo hannun mu."
"Haka nan kuma duk da gwamnonin G5 sun cika a kan matsayarsu ta dole Ayu ya yi murabus, kowa ya san abinda suka dogara da shi, mai yuwuwa don sun faɗi a zaɓen fidda gwani ne amma da mun yi hasashen abinda ka iya faruwa."

Kara karanta wannan

Fitaccen Mamban APC Ya Magantu Kan Sauya Shekar Tsohon Gwamnan PDP Zuwa APC

"Abinda ya kamata shugaban PDP ya yi shi ne, idan har murabus ɗinsa zai taimaki jam'iyya ta ci zaɓe me zai hana? Ban san meyasa Ayu ya kafe dole sai ya zauna ba."

Abba Kabir Yusuf Ya Yi Karin Haske Kan Biyayyar Da Yake Wa Kwankwaso

A wani labarin na daban kuma Gwamna Abba Gida-Gida na jihar Kano ya kare kansa game da biyayyar da yake wa tsohon gwamna Sanata Rabiu Kwankwaso.

Abba Gida-Gida ya ce gogewar Kwankwaso a matsayin wanda ya riƙe kujerar gwamna, Sanata da Minista ya cancanci zama jogoran da za'a yi wa biyayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262