Tsohon Ministan Jonathan Ya Ki Amsar Babban Mukami Na Duniya Saboda Nadin Tinubu
- Muhammad Pate, tsohon karamin ministan lafiya, na iya samun shiga majalisar shugaban kasa Bola Tinubu
- Hakan ya bayyana a fili bayan Pate ya ki amsar tayin shugabancin kungiyar GAVI, yana mai cewa an bukaci ya dawo kasar domin bayar da gudunmawa a kasarsa ta haihuwa
- Pate ya yi aiki a matsayin karamin ministan lafiya karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tsakanin 2011 da 2013
Tsohon karamin ministan lafiya, Muhammad Pate, na iya zama daya daga cikin ministocin shugaban kasa Bola Tinubu bayan an yi wasu sabbin sanarwa a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni.
Har yanzu shugaban kasa Tinubu wanda ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayu bai mika jerin sunayen ministocinsa ga majalisar dokokin kasa ba kamar yadda doka ta bayyana, jaridar Premium Times ta rahoto.
A bisa ga doka, ana sa ran shugaban kasar ya aika jerin sunayen mutanen da yake so zuwa majalisa cikin kwanaki 60 da kama aiki amma har yanzu bai aikata haka ba bayan wata guda da rantsar da shi.
Dalilin da yasa ministan Jonathan zai samu shiga majalisar Tinubu
Yiwuwar Pate ya zama ministan shugaban kasa Tinubu ya fito fili ne bayan kungiyar GAVI ta sanar da shawarar da tsohon ministan ya yanke na ajiye nadin da ta yi masa a matsayin shugabanta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Leadership ta rahoto cewa an shirya Pate zai kama aiki a matsayin shugaban GAVI a ranar 3 ga watan Agusta amma ya sanar da kungiyar cewa "ya yanke shawara mai wahala na amsa tayin komawa kasarsa Najeriya tare da bayar da gudunmawarsa."
Dalilinsa na kin karbar mukamin ya sa ana ta rade-radin cewa watakila an ware masa kujera a sabuwar majalisar Tinubu.
Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi
Pate ya yi aiki a matsayin karamin ministan lafiya tsakanin 2011 da 2013 karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Tattalin Arziki: Shehu Sani Ya Bukaci Tinubu Ya Binciki Buhari, Tsoffin Ministoci Da Sauransu
A wani labari na daban, tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana dalilin da yasa akwai bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministocinsa da tsoffin shugabannin tsaro na gwamnatinsa.
Sani ya ce ya kamata shugaban kasa Tinubu ya binciki laifukan tattalin arziki da aka tafka a karkashin gwamnatin Buhari cike da karfin gwiwa.
Asali: Legit.ng