Shugaban Majalisar Dattawa, Godwin Akpabio, Ya Yi Nadin Farko Bayan Cin Zabe
- Sanata Godswill Akpabio ya yi sabbin manyan naɗe-naɗe guda biyu karon farko tun bayan lashe zaɓen shugaban majalisar dattawa
- Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya naɗa shugaban ma'aikatansa da kuma mataimaki ranar Litinin 26 ga watan Yuni
- Yayin rantsar da majalisa ta 10, Sanata Akpabi ya samu nasara da kuri'a mafi rinjaye bayan fafata zazzafan zaɓe da Abdul'aziz Yari
FCT Abuja - Sabon shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi sabbin naɗe-naɗe karon farko tun bayan samun nasara a majalisar tarayya ta 10.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sanata Akpabio ya amince da naɗin Barista Sylvester Okonkwo, a matsayin shugaban ma'aikatansa.
Haka nan ya amince da naɗin Saviour Enyiekere, wanda ya hito daga ƙaramar hukumar Ika, jihar Akwa Ibom a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatansa.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ta fito daga ofishin midiya na shugaban majalisar dattawan Najeriya ranar Litinin, 26 ga watan Yuni, 2023, kamar yadda Tribune ta kawo a rahotonta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taƙaitaccen tarihin sabon shugaban ma'aikatan Akpabio
Sabon shugaban ma'aikatan Akpabio, Barista Okonkwo, ya halarci makarantar Dennìs Memorial Grammar School kuma kuma tsohon ɗalibi ne a jami'ar Najeriya, Enugu.
Ya kammala digirinsa na farko a jami'ar, inda ya karanci ilimin shari'a (Law). Haka nan ya fito daga ƙauyen Ojoto, ƙaramar hukumar Idemili ta kudu a jihar Anambra, Kudu maso Gabashin Najeriya.
Har zuwa yau da aka naɗa shi wannan muƙamin, Okonkwo, shi ne babban shugaba CEO na kamfanin sadarwa da harkokin intanet Chinto Technologies Limited.
Takaitaccen tarihin mataimakin shugaban ma'aikatan Akpabio
A ɗaya ɓangaren kuma Saviour Enyiekere ya yi karatu a jami'ar Kalaba kuma shi ne mataimakin daraktan yaƙin neman zaben Sanata Akpabio a zaɓen 2023.
Ya riƙe manyan muƙamai a siyasa daga cikinsu ya riƙe shugaban ƙaramar hukumar Ika tsawon zango biyu da babban mataimaki na musamman a gwamnatin Akwa Ibom.
Sifetan Yan Sanda Ya Sa Labule da Kwamandojin Rundunar Yan Sanda a Abuja
A wani rahoton na daban kuma Muƙaddashin IGP ya shiga ganawa da kwamandoji 79 na rundunoni daban-daban a hukumar 'yan sanda.
Dukkan mataimakan sifetan 'yan sanda na ƙasa daga shiyyoyi Shida da ake da su a Najeriya (DIG) sun halarci taron na yau Litinin, 26 ga watan Yuni, 2023.
Asali: Legit.ng