Tinubu Ya Sauyawa Filayen Jiragen Sama Suna Zuwa Sunayen Buhari, Sanusi, Da Wasu Mutane 13
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauyawa wasu filayen jiragen sama na Najeriya sunaye zuwa sunayen wasu fitattun ‘yan Najeriya.
An sanar da sauya sunayen filayen jiragen saman ne a cikin wata takarda da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayyar Najeriya ta fitar.
Sanarwar dai na dauke da kwanan watan 1 ga watan Yunin shekarar 2023, sannan tana dauke da sa hannun Misis Joke Olatunji, daraktar ayyuka ta filayen jiragen sama a ranar Litinin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Sanarwar ta bayyana sauyin sunayen da Shugaba Tinubu ya yi, a matsayin wani bangare na garambawul a bangaren sufurin jiragen sama.
An sauya sunayen filayen jiragen saman zuwa sunayen wasu manyan ‘yan Najeriya
An canza sunan filin jirgin sama na Maiduguri da sunan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma, an sauya sunan filin jirgin sama na Fatakwal da sunan marigayi dan kishin kasa, Obafemi Awolowo, a yayin da filin jirgin saman Nasarawa, ya ci sunan marigayi Shehu Usman Dan Fodio wanda ya kafa Daular Sokoto.
Haka zalika, an sauya sunan filin jirgin sama na Benin da sunan marigayi Oba na Benin, Oba Akenzua II, filin jirgin sama na Ebonyi da sunan tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Chuba Okadigbo, da filin jirgin sama na Ibadan da sunan tsohon Firimiyan Yamma, Ladoke Akintola.
Cikakken jerin sunayen mutane 15 da aka sauya sunayen filayen zuwa sunayensu
Ga cikakken jerin sunayen mutane 15 din aka sauya sunayen filayen jiragen sama zuwa sunayensu, kamar yadda yake a wani rahoto na gidan talabijin na Channels.
1. Filin Jirgin sama na Akure – Olumuyiwa Bernard Aliu
2. Filin Jirgin sama na Benin – Oba Akenzua II
3. Filin jirgin sama na Dutse – Muhammad Nuhu Sanusi
4. Filin Jirgin sama na Ebonyi – Chuba Wilberforce Okadigbo
5. Filin Jirgin sama na Gombe – Birgediya Zakari Maimalari
6. Filin Jirgin sama na Ibadan – Samuel Ladoke Akintola
7. Filin jirgin sama na Ilorin – Janar Tunde Idiagbon
8. Filin Jirgin sama na Kaduna – Hassan Usman Katsina
9. Filin Jirgin sama na Maiduguri – Janar Muhammadu Buhari
10. Filin Jirgin sama na Makurdi – Joseph Sarwuan Tarka
11. Filin Jirgin sama na Minna – Mallam Abubakar Imam
12. Filin Jirgin sama na Nassarawa – Sheikh Usman Dan Fodio
13. Filin Jirgin sama na Osubi – Alfred Diete Spiff
14. Filin jirgin sama na Fatakwal – Obafemi Jeremiah Awolowo
15. Filin Jirgin sama na Yola – Lamido Aliyu Mustapha
Tinubu ya bayyana yadda wani sojan Amurka ya tafka masa mari
Legit.ng a baya ta kawo muku wani labari kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bayyana cewa wani sojan kasar Amurka ya taba sharara masa mari.
Tinubu ya bayyana cewa hakan ta faru ne a lokacin da yake tukin taksi a kasar ta Amurka, domin ya samu kudaden daukar dawainiyar karatunsa.
Asali: Legit.ng