Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana Kan Jerin Sunayen Ministocin Tinubu
- Masu fatan ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen ministocinsa cikin yan kwanakin nan za su yi hakuri su cigaba da jira
- Hakan na zuwa ne bayan mai magana da yawun Shugaban kasar Dele Alake ya fada wa yan jarida a Abuja cewa hasashen da ake ni game da fitar da ministocin yan kwanakin nan ba gaskiya bane
- Ya ce kawo yanzu Shugaban kasar bai tattara sunayen wadanda zai nada minista ba amma idan an yi hakan zai sanar da al'ummar kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - A karshe fadar shugaban kasa ta yi martani kan hasashen da ake ta yi gamen na cewa an gama tattara sunayen ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Da ya ke martani kan wannan hasashen, Dele Alake, mai magana da yawun shugaban kasa Tinubu, ya ce ba a tattara jerin sunayen ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai magana da yawun shugaban kasar ya yi wannan ikirarin ne a ranar Alhamis 6 ga watan Yuli a Abuja yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi.
Abin da Dele Alake ya bayyana game da sunayen ministocin Tinubu
Kamar yadda Premium Times ta rahoto, ya ce:
"Babu alamar gaskiya cikin wadannan abubuwan," Mista Alake ya ce game da jita-jita kan sunayen ministoci.
"Idan Shugaban kasar ya shirya kuma ya natsu, kune na farko da za ku san abin da ya ke son yi."
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng