Gagarumin Baraka Ya Kunno Kai a Majalisar Dattawa: Sanatocin APC 22 Na Shirin Sauya Sheka Zuwa PDP

Gagarumin Baraka Ya Kunno Kai a Majalisar Dattawa: Sanatocin APC 22 Na Shirin Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Akalla sanatoci 22 ne ke shirin sauya sheka daga APC zuwa PDP lamarin da zai iya haifar da gagarumin sauyi a majalisar dattawa, kamar yadda rahotanni suka nuna
  • Idan har hakan ya kasance, PDP a matsayinta na babbar jam'iyyar adawa za ta zama mafi rinjaye a majalisar, da karin kujeru zuwa 58 inda kujerun APC zai ragu zuwa 37
  • Wata majiya da ba a bayyana ba ta kuma bayyana shirin kalubalantar sakamakon zaben Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, kan zargin magudi

Abuja - Wani rahoton Daily Sun ya bayyana cewa akwai yunkuri da ake yi na haifar da gagarumin matsala a majalisar dattawa, inda sanatocin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ke shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Idan aka cimma wannan manufa, PDP, babbar jam'iyyar adawa za ta zama mai rinjaye a majalisar dattawan.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi Mai: Kungiyar Masu 'POS' Sun Sanar Da Sabon Farashin Cire Kudi, Suna Fatan Yan Najeriya Za Su Rungumi Canjin

Sanata Yari da Sanata Akpabio
Gagarumin Baraka Ya Kunno Kai a Majalisar Dattawa: Sanatocin APC 22 Na Shirin Sauya Sheka Zuwa PDP Hoto: Mansur Isah Buhari, Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Daga cikin yan majalisar dattawa 102, da ke zauren, APC ke rike da kujeru 59, PDP na da kujeru 36, yayin da Labour Party (LP), Democratic Party (SDP), New Nigeria People's Party (NNPP), Young Progressives Party (YPP), da All Progressives Grand Alliance (APGA) ke da kujeru 8, 2, 2, 1, da 1 kowannensu.

Idan Sanatocin APC 22 suka aiwatar da barazanarsu, zai kara adadin sanatocin PDP zuwa 58 sannan ya rage na APC zuwa 37.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sanatocin APC ke kulla-kulla don nada Yari shugaban majalisar dattawa

An yi zargin cewa sanatocin na APC 22 sun yanke shawarar hada karfi tare da takwarorinsu wadanda ke biyayya da Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari.

Ku tuna cewa Yari ya yi takarar kujerar shugaban majalisar dattawa amma ya sha kaye a hannun Sanata Godswill Akpabio.

Majiyar da ba a bayyana sunanta ba ta kuma ce sanatocin sun yi ganawa daban-daban a Abuja da Landan, inda suka tabbatar da shawararsu na sauya sheka zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Fitaccen Mamban APC Ya Magantu Kan Sauya Shekar Tsohon Gwamnan PDP Zuwa APC

Domin cimma kudirinsu, an tattaro cewa sanatocin PDP sun yarda su mika mukamin shugaban majalisar dattawa wanda Sanata Akpabio ke rike da shi a yanzu ga daya daga cikin sanatocin 22 da makusantan Yari da za su sauya sheka zuwa jam'iyyar, da kuma mukamin mataimakin shugaban majalisar datawan.

A bangaren sanatocin PDP, jam'iyyar za ta karbi shugabancin masu rinjaye a majalisa, shugaban masu tsawatarwa da mataimakin shugaban masu tsawatarwa a majalisar, inji majiyar tana mai cewa kungiyar Yari ta sha alwashin aiki tare da su cin aminci.

Wasu rukunin sanatoci na shirin kalubalantar zaben Akpabio

A halin da ake ciki, Daily Sun ta kuma rahoto cewa wasu sanatocin arewa maso yamma da ba a ambaci sunansu ba sun yanke shawarar kalubalantar sakamakon zaben Akpabio a kotu.

Kungiyar ta yi zargin cewa takardun da aka yi amfani da su a zaben ya kamata su kasance zaben sirri amma aka yi magudi.

Kara karanta wannan

Manyan Jiga-Jigan PDP da Dubannin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC Ana Tunkarar Zaɓe a Jihar Arewa

Abdulaziz Yari: 'Wasu Takwarorina Sun Ci Amanata Yayin Zaben Shugaban Majalisa Ta 10'

A baya mun ji cewa Sanata Abdulaziz Yari, ya ce yana ji kamar an yaudare shi a zaɓen shugabancin Majalisar ta 10 da ya gabata.

A yayin ƙaddamar da majalisar ta 10, sanatoci sun zaɓi sabon shugaba, inda Sanata Godswill Akpabio ya zama shugaban Majalisar Dattawan da ƙuri’u 63, a yayin da abokin hamayyarsa Abdulaziz Yari ya samu ƙuri’u 46.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng