“Takardar Tinubu Na Shiga Jami’ar Chicago Na Dauke Da Jinsin Mace,” Inji Shaida
- An samu sabon al'amari dangane da shari'ar PDP, dan takararta Atiku Abubakar da Bola Tinubu a kotun zaben shugaban kasa
- Shaidan da ke wakiltan PDP da Atiku a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, ya bayyana cewa takardar Tinubu na samun gurbin karatu a jami'ar Chicago yana dauke da jinsin mace
- Jam'iyyar PDP ta gabatar da takardun ta hannun shaidansu, Mike Enahoro-Ebah, wanda ya kasance lauya mai zaman kansa
Shaida mai wakiltan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Atiku Abubakar ya yi wani fallasa mai ban mamaki a kotun zabe a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
Shaidan Atiku ya sanar da kotun zaben shugaban kasar da ke zama a Abuja cewa takardar neman gurbin karatu a jami'ar Chicago da kwalejin South West ta yi da sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana shi a matsayin mace, Nigerian Tribune ta rahoto.
Takardar samun gurbin karatun Tinubu na dauek da jinsin mace, PDP ta dage
Jam'iyyar PDP ta gabatar da takardan, tare da sauran takardu domin tabbatar da zarge-zargen a wani shari'ar hadin gwiwa da ke kalubalantar ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake jagorantar shaidan masu kara na 27, Mista Mike Enahoro-Eba, domin ya ba da shaida a kotu, babban lauyan masu kara, Cif Chris Uche (SAN), ya mika takardun ta hannun shaidan, wanda ya kasance mai rajin kare hakkin dan adam mazaunin Abuja kuma lauya mai kare muradan jama'a.
Saboda haka kotun ta amshi takardun sannan ta sanya su a matsayin hujjoji.
"A duba lamarinmu": Yan Abuja sun roki shugaban kasa Tinubu da ya basu minsitan Abuja
A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa yan asalin Abuja sun mika wani babban bukata da suke neman a biya masu a gaban shugaban kasa Bola Tinubu inda suka roki ya basu kujerar ministan babban birnin tarayya.
Yan asalin yankin wadanda suka ce an dade ana kwararsu sun ce babu yadda za a yi a ci gaba da dauko masu bakin haure domin jibantar lamuransu.
Asali: Legit.ng