Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi a Benue

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi a Benue

  • Jam'iyyar PDP ta caccaki gwamnatin APC karkashin jagorancin gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai
  • A wata sanarwa da kakakin PDP reshen jihar ya fitar, jam'iyyar ta soki matakin dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23
  • PDP ta ce gwamna da majalisar dokokin Benuwai sun shiga ruɗani domin tuni Kotu ta hana dakatar da ciyamomin

Benue - Jam'iyyar PDP reshen jihar Benuwai ta maida martani ga gwamna Hyacinth Alia game da matakin da ya ɗauka na dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majalisar dokokin jihar Benuwai ta dakatar da ciyamomin domin ba da cikakkiyar damar gudanar da bincike kan zargin wawure kuɗaɗe.

PDP ta maida martani ga gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai.
Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi a Benue Hoto: Hyacinth Alia
Asali: UGC

PDP ta caccaki gwamna Alia

Yayin martani kan haka a wata sanarwa, kakakin PDP, Bemgba Iortyom, ya ce gwamna Alia da majalisa karkashin jagorancin APC duk sun shiga ruɗani.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan PDP a Arewa Zai Fara Ciyo Bashin N15bn Ƙasa da Wata 1 Da Hawa Mulki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashin sanarwa da kakakin PDP ya fitar ya ce:

"Yayin da giyar mulki ta fara ruɗar na kan madafun iko, a ranar 14 ga watan, Yuni, 2023, gwamna ta hannun shugaban ma'aikatansa ya aike da buƙatar dakatar da shugabannin kananan hukumomi ga majalisa."
"Ya fake da sunan gudanar da bincike kan kuɗin shiga da waɗanda suka fita a baitulmalin kananan hukumomi daga watan Fabrairu zuwa Afrilu, 2023, ya nemi majalisa ta yi bincike kuma ta bada shawarar da ya dace a rahoto."
"Bayan muhawara kan sakon gwamna a zauren majalisa ranar 20 ga watan Yuni, 2023, majalisa ta kafa kwamitin mutum 3 da zasu gudanar da bincike kuma su dawo mata da rahoto cikin mako biyu."

Wannan mataki ya saɓa wa umarnin Kotu

Mista Iorytom ya ƙara da cewa wannan matakin ya saɓa wa umarnin Kotu mai cikakken iko, wacce ta haramta wa gwamnatin jiha dakatar da zaɓaɓɓun shugabanni a matakin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Bakin Aiki Bayan Wani Shugaban Makaranta Ya Aikata Abu 1

Ya bayyana cewa gwamnatin ba ta san komai ba ɓalle ta daukaƙa ƙara kan wannan hukunci da Kotu ta riga ta yanke, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Majalisar Dokokin Jihar Filato Ta Amince Wa Gwamna Muftwang Ya Karbo Bashin N15bn

A wani rahoton na daban kuma Gwamnan jihar Filato ya samu amincewar majalisar dokoki na karɓo bashin naira biliyan N15bn.

Gwamnan ya aike da takardar bukatar neman karɓo wannan bashin ga majalisar dokokin jihar ne da nufin amfani da kuɗin wajen biyan albashin ma'aikata da kuma siyo kayan noma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262