Sokoto: Gwamna Ahmad Aliyu Ya Yi Manyan Nade-Nade a Gwamnatinsa

Sokoto: Gwamna Ahmad Aliyu Ya Yi Manyan Nade-Nade a Gwamnatinsa

  • Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato ya naɗa mutane 7 a manyan muƙamai daban-daban ranar Laraba, 21 ga watan Yuni
  • Daga cikin naɗin da gwamnan ya yi harda sabon sakataren gwamnatin jihar da shugaban ma'aikatan gidan gwamnati
  • Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan ya kori manyan Sakatarorin ilimi a kananan hukumomi 23 da ke jihar Sakkwato

Sokoto - Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya zaɓi mutum 7 ya naɗa su a manyan muƙamai kala daban-daban ciki harda sakataren gwamnatin jiha (SSG)

Wannan naɗe-naɗe na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Abubakar Bawa, ya aike wa jaridar Leadership jiya Laraba, 21 ga watan Yuni.

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu.
Sokoto: Gwamna Ahmad Aliyu Ya Yi Manyan Nade-Nade a Gwamnatinsa Hoto: leadership
Asali: UGC

Sabbin naɗe-naɗen da gwamna Aliyu ya yi

A cewar sanarwan, Gwamna Aliyu ya amince da naɗin Alhaji Muammadu Bello Sifawa a matsayin sakataren gwamnatin jiha (SSG) da kuma Alhaji Aminu Haliru Dikko a matsayin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati (CoS).

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Bakin Aiki Bayan Wani Shugaban Makaranta Ya Aikata Abu 1

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran waɗanda gwamnan ya naɗa sun haɗa da, Alhaji Gandi Umar, a matsayin babban mai ba da shawara kan harkokin shugabanci da Alhaji Husaini Umar Gorau, a matsayin mataimaki na musamman (P.A).

Sai kuma Honorabul Bello Yahaya Wurno a matsayin babban mai taimaka wa gwamna kan harkokin cuɗanya da gwamnatoci da Faruk Labbo, mai taimaka wa kan harkokin cikin gida.

Haka zalika mai girma gwamnan Sakkwato ya naɗa Faruk Ahmad Shuni, a matsayin babban mai ba da shawara kan harkokin tsare-tsare, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Har yanzu akwai ƙara kan zaben Aliyu a gaban Kotu

Wannan naɗe-naɗen na zuwa ne yayin da Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben gwamnan jihar Sakkwato ta fara sauraron shaidu daga ɓangaren masu ƙara.

A zaman Kotu na jiya Laraba, shugaban makarantar Firamare ta Sabon Birni ya gabatar da takardun bayanai da suka tabbatar mataimakin gwamna ba makarantar ya yi ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Haramta Ayyukan 'Yan Acaba a Babban Birnin Jiha, Ya Faɗi Dalilai

Gwamna Aliyu Ya Kori Sakatarorin Ilimi Na Kananan Hukumomi 23 a Sakkwato

A ɗazu mun kawo muku rahoton cewa Gwamna Aliyu na jihar Sakkwato ya sallami Sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 daga aiki.

Ya kuma umarci baki ɗaya Sakatarorin da korar ta shafa su miƙa jagorancin hukumomin ilimin ga manyan ma'aikatan Ofis ɗinsu a kananan hukumomin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262