Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince da Naɗin Kwamishinoni 16 Cikin 19

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince da Naɗin Kwamishinoni 16 Cikin 19

  • Kwamishinoni 16 cikin 19 da gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura wa majalisar dokokin Kano sun tsallake matakin tantancewa
  • A zaman yau Alhamis, majalisar ta amince da naɗin kwamishinonin 16 amma ta tsallake mutum uku
  • Biyu daga cikin ragowar guda ukun sun tafi aiki Hajji ne shiyasa ba'a tantance su ba yayin da ɗayan kuma shi ne mataimakin gwamna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance tare da amincewa da kwamishinoni 16 cikin 19 da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya aiko mata.

Majalisar ta amince da naɗin kwamishinonin a matsayin mambobin majalisar zartarwa ta jihar Kano bayan sun tsallake tantancewa a zaman majalisa na ranar Alhamis.

Zauren majalisar dokokin jihar Kano.
Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince da Naɗin Kwamishinoni 16 Cikin 19 Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Rahoton Daily Trust ya kawo cewa gwamna Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya tura sunayen kwamishinoni 19 ga majalisa ranar Talata da ta gabata.

Kara karanta wannan

Ya Cika Alkawari: Gwamnan PDP Ya Naɗa Sabbin Kwamishinoni 7, Ya Tura Sako Ga Majalisa

Bayan kammala tantance mutane 16 cikin 19, majalisar ta amince tare da tabbatar da sabbin kwamishinonin a kudirin da shugaban masu rinjaye, Lawal Hussaini, mai wakiltar mazaɓar Dala ya gabatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa majalisar ta tsallake ragowar mutum 3?

Legit.ng Hausa ta gano cewa biyu daga cikin ragowar kwamishinoni 3 da majalisar ta tsallake, Hajiya Aisha Saji da Sheikh Tijjani Auwal, suna ƙasa mai tsarki yanzu haka suna aikin Hajji.

Sai dai majalisar ta umarci mutanen biyu da zaran sun kammala sun dawo gida Najeriya, su gaggauta gabatar da kansu a gabanta domin tantancewa.

Majalisar ta cire na ukun kuma na karshe da ba'a tantance ba, kwamaret Aminu Abdussalam, saboda kasancewarsa mataimakin gwamnan Kano mai ci, kamar yadda PM News ta tattaro.

A cewar majalisar tunda ya riga ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin mataimakin gwamna, ba bu buƙatar sai an tantance shi gabanin ya riƙe mukamin kwamishina.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 35 da Wasu Hadimai da Ya Naɗa

Jerin waɗanda majalisar da amince da su a zamanta

Waɗanda suka tsallake tantancewar majalisar sun haɗa da, Ali Makoɗa, tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Ganduje da shugaban NNPP na Kano, Umar Doguwa.

Sai kuma tsoffin yan majalisar tarayya, Nasiru Sule Garo da Haruna Dederi, da kuma tsohon daraktan sadarwa na Sanata Rabiu Kwankwaso, Baba Dantiye.

Sauran su ne, Abubakar Labaran Yusuf, Danjuma Mahmoud, Musa Shanono, Abbas Sani Abbas, Ladidi Garko, Marwan Ahmad, Dr. Mahmoud Diggol, Adamu Aliyu Kibiya, Dr. Yusuf Kofar Mata, Hamza Safiyanu, da Tajo Usman Zaura.

Kashim Shettima Ya Sa Labule da Bill Gates, Gangote da Wasu Gwamnoni a Villa

A wani labarin kuma Mataimakin shugaban kasa ya shiga ganawar sirri da Bill Gates, Aliko Ɗangote da wasu gwamnonin Najeriya a fadar shugaban ƙasa.

Taron, wanda aka fara da misalin karfe 11:43 na safiyar Alhamis, 22 ga watan Yuni, na cikin ɓangaren ayyukan da ziyarar Bill Gates a Najeriya da Jamhuriyar Nijar ta ƙunsa.

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262