Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Mayar Da Muhuyi Magaji Kan Muƙaminsa Na Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Mayar Da Muhuyi Magaji Kan Muƙaminsa Na Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa

  • Gwamna mai ci na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida, ya aiwatar da wani gagarumin aiki
  • Gwamnan ya amince da mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, kan matsayin Shugaban Hukumar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa (PCACC)
  • Hukumar PCACC, hukuma ce da ke karɓar ƙorafe-ƙorafe gami da bima waɗanda aka dannewa haƙƙi kadin haƙƙinsu a jihar Kano

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

KanoGwamna Abba Kabir Yusuf a ranar Laraba, ya amince da mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, kan matsayin shugaban Hukumar Karɓar Korafe-korafen Jama’a Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (PCACC) ta jihar Kano.

Maidowar da Abba ya yi wa Rimin Gado, tana nufin zai samu damar kammala wa'adinsa na shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawar kamar yadda NTA News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida Ya Karya Alkawari, Ya Jawo Yaronsa Ya Ba Shi Mukami a Gwamnati

Abba ya mayar da Muhyi kan muƙaminsa
Abba Gida Gida ya mayar da Muhyi Magaji Rimingado kan muƙaminsa. Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa
Asali: Facebook

Sanarwar dai ta fito ne ta hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban sakataren yaɗa Labarai na gwamnatin Kano.

Tsohon gwamnan Kano ne ya dakatar da Muhyi

Idan dai za a iya tunawa, gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Ganduje ce ta dakatar da Muhyi Magaji daga kan muƙamin nasa a can baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An umarci Muhyi da ya fara aiki nan take, a cewar sanarwar da gwamnan ya fitar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni.

Gwamnatin Kano ta yi martani kan batun da ake yaɗawa na dawo da Sanusi a matsayin Sarkin Kano

A wani labarin makamancin wannan, Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa har yanzu bai yanke shawara kan mayar da Muhammad Sanusi matsayin Sarkin Kano ba.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, gwamnan ya mayar da martani ne dangane da raɗe-raɗin da ake yi na cewa gwamnatin jihar za ta sauke dukkan sarakunan da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta naɗa.

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

Wani rahoto na baya bayan nan, ya tabbatar da cewa majalisar dokokin jihar za ta zauna a kan lamarin tare da gabatar da ƙudirin a zaman da majalisar za ta yi a gaba.

Abba ya nemi kwamishinoninsa su bayyana abinda suka mallaka

A wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nemi kwamishinonin da zai naɗa da su bayyana dukkanin kadarorin da suka mallaka gabanin a tabbatar da su.

Abba ya sharɗanta cewa dole ne kowanensu ya bi ƙa'ida, wajen bayyana kadarorinsa gaban hukumar ɗa'ar ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng