Gwamna Nwifuru Na Ebonyi Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 35 da Wasu Hadimai
- Sabbin kwamishinoni 35 sun karɓi shahadar kama aiki daga wurin gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ranar Talata
- Gwamnan ya umarci su haɗa karfi wajen ciyar da jihar zuwa gaba domin ba bu wanda ya ɗauko saboda siyasa
- Ya kuma gargaɗe su da cewa ba zai lamurci gazawa ba, duk wanda ya tsaya sakarci zai sauke shi ya ɗora wani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Enugu - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, a ranar Talata, ya rantsar da sabbin kwamishinoni akalla 35 da ya naɗa a matsayin mambobin majalisar zartarwa.
Sabbin kwamishinonin sun yi rantsuwar kama aiki ne a zauren majalisar zartarwa da ke fadar gwamnatin jihar Ebonyi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Yayin wannan bikin, Gwamnan na jam'iyyar APC ya buƙace su da su kawo sabbin abubuwa da dabarun sauke nauyi, inda ya faɗa musu cewa ya naɗa su muƙamai ne ba dan siyasa ba.
Haka nan kuma gwamna Nwifuru ya rantsar da shugaban ma'aikatansa, Farfesa Emmanuel Echiegu, da mataimaki, Injiniya Timothy Nwachi, da mashawarta na musamman da sauransu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ba zan lamurci sakarci ba - Gwamna Nwifuru
Da yake jawabi ga baki ɗaya waɗanda ya bai wa mukamai, gwamnan ya roki su haɗa hannu wuri ɗaya domin kai jihar tudun mun tsira, inda ya ce gwamnatinsa ba zata lamurci sakarci ba.
A rahoton jaridar Guardian, gwamna Francis Nwifuru ya ce:
"Kamar yadda kuka sani wannan kiran aiki ne, yayin da nake taya ku murna, ina gargaɗinku ku ɗauki wannan aiki da muhimmanci, kuma wannan naɗin da aka muku ba wai don siyasa bane."
"Da zaran na gano gazawa a ofishinka, nan take zan sallameka kuma ba zan sake dawo da kai ba. Jiharmu a shirye take tana jiran sabon salon shugabancin da muka zo da shi, don haka dole mu nuna musu zamu iya."
Wasu daga cikin mutanen da suna dafi mukamin kwamishina
Wasu daga cikin kwamishinonin da gwamnan ya naɗa sun kunshi;
Ma'aikatar ayyuka da sufuri, Engr Lebechi Mbam; ma'aikatar kudi, Dakta Leonard Uguru; ma'aikatar filaye da ƙasa, Dakta Matthew Nwobashi; da ma'aikatar ilimin gaba da sakandire, Farfesa Omari Omaka (SAN).
Ma'aikatar raya kasuwa da tashoshi, Farfesa Nwogo Obasi; ma'aikatar samar da ayyuka, Elijah Oko-Udu; tsaron cikin gida, Prince Etta Ude; mahalli, Honorabul Victor Chukwu; yaɗa labarai da wayar da kai Jude Okpor da sauransu.
Gwamna Ya Ɗau Zafi, Ya Umarci Dukkan Kwamishinoninsa Su Bayyana Dukiya Nan Take
A wani rahoton na daban Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci baki ɗaya kwamishinonin da ya zaɓa su gaggauta bayyana abinda suka mallaka.
Abba Gida-Gida ya lashi takobin cewa ba zai rantsar da duk wanda ya yi fatali da Fam ɗin bayyana dukiyar da ka mallaka ba.
Asali: Legit.ng