Kakakin Majalisar Dokokin Ogun Ya Yi Tazarce Duk da Tuhumar Wawure N2.5bn
- Shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, ya samu nasarar tazarce kan kujerarsa bayan kai ruwa rana yau Talata
- Rahoto ya nuna cewa an yi dirama a majalisar, wanda ta tilastawa ɗayan ɗan takarar janye wa saboda matsin lamba
- Kakakin majalisar ya samu wannan nasarar duk da shari'ar da yake fama da ita wacce ake zargin ya wawure wasu kuɗi N2.5bn
Ogun - Mambobi sun sake zaben kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Honorabul Olakunle Oluomo a karo na biyu duk da tuhumar da ake masa ta sama da faɗi da biliyan N2.5bn.
Kakakin majalisar ya sake zarcewa kan muƙamin ne bayan shafe awanni hudu ana dirama yayin zaben sabon shugaban majalisar dokokin Ogun wacce APC ke mulki.
Daily Trust ta ruwaito cewa yayin zaman zaɓen, sai da aka matsa wa babban mai neman kujerar, Oludaisi Elemide, ya janye bisa tilas daga ƙarshe kafin Olakunle ya iya samun nasara.
Elemide, mai goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Aremo Olusegun Osoba, a mintunan karshe ya janye daga neman zama kakakin majalisa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda zaman majalisa ya gudana yau Talata
An ce tashin hankali da rashin tabbas ne suka mamaye bikin rantsar da sabuwar majalisar dokokin jihar Ogun ta 10, lamarin da ya sa tun farko aka ɗage rantsarwan zuwa yau.
Rahoton The Nation ya tattaro cewa har zuwa lokacin fara zaman majalisar da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Talata, Oluomo, wanda gwamna Dapo Abiodon ke goyon baya ba shi da tabbas.
Kakakin majalisa ta 9 da ta gabata kuma sabo, Oluomo, na fama da shari'ar biliyan N2.5bn waɗanda ake zargin kuɗin majalisar ne ya karkatar da su.
Mace ta zama mataimakiya
Bugu da ƙari, mambobin majalisar sun zaɓi mamba mace, Misis Ajayi Bolanle, mai wakiltar mazaɓar Yewa ta kudu a matsayin mataimakiyar shugaban majalisa.
Abba Gida Gida Ya Aike da Sunayen Kwamishinoni 19 Ga Majalisar Dokokin Kano
A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa sabbin kwamishinoni 19 kuma ya tura sunayensu ga majalisar dokoki domin tantancewa.
Kakakin majalisa, Isma'il Falgore, ya karanta sunayan kwamishinonin da mai girma gwamna ya aiko a zaman ranar Talata.
Asali: Legit.ng