Kotun Sauraron Karar Zabe Ta Yi Fatali Da Karar PDP Kan APC

Kotun Sauraron Karar Zabe Ta Yi Fatali Da Karar PDP Kan APC

  • Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Ogun ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar kan APC
  • Jam'iyyar ta PDP da dan takararta, Oladipupo Adebutu, suna kallubalantar nasarar Dapo Abiodun ne a zaben ranar 18 ga watan Maris a jihar
  • Adebutu ya yi ikirarin cewa jam'iyyar ta APC da dan takararta, Gwamna Abiodun, sun siya kuri'u yayin zaben

Jihar Ogun - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Osun a ranar Litinin 19 ga watan Yuni ta yi fatali da karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta shigar kan jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun na ranar 18 ga watan Maris, Oladipupo Adebutu, ya yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ta siya kuri'u, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sallami Hafsoshin Tsaro da IGP Daga Aiki, Ya Naɗa Sabbin Da Zasu Maye Gurbinsu

Kotu ta yi watsi da karar kallubalantar nasarar APC da PDP ke yi a Ogun
Kot Ta Yi Fatali Da Karar PDP Kan APC. Hoto: PDP Update
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

PDP ta zargi APC da siyan kuri'u

A karar da Adebutu da jam'iyyar PDP suka shigar a ranar 6 ga watan Afrilu mai lamba EPT/OG/GOV/03/2023, an kallubalanci nasarar Gwamna Dapo Abiodun kan rashin bin dokokin zabe da kuma zargin aikata cin hanci yayin zaben.

Mai shari'a Hamidu Kunaza ne ya jagoranci tawagar alkalai uku a daya cikin sauraron korafin sharar fage a ranar 13 ga watan Yuni.

Wole Olanipekun (SAN), shugaban lauyoyi masu kare gwamna, cikin takardar da ya shigar ya kallubalanci amsar da wanda suka shigar da karar suka bada mai dauke da kwanan wata 22 ga watan Mayu na zargin siyan kuri'u da aka yi wa (Abiodun) yayin zaben.

APC da PDP na cece-kuce kan batun siyan kuri'u a kotu

Tawagar alkalai masu kare Abiodun kan suma sun tada batun zargin siyan kuri'a da ake musu kan Adebutu da jam'iyyar PDP a kararsu ta farko, kamar yadda suma ake musu zargin siyan kuri'un.

Kara karanta wannan

Alkalan Kotun Karar Zaben 2023 Sun Yi Fatali da Rokon Lauyoyin APC, Bola Tinubu

Hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Ogun dai ta ayyana Abiodun a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan a ranar 19 ga watan Maris.

Tinubu Ya Nada Sabbin Masu Bada Shawara 4 Kafin Ya Tafi Faransa

A wani rahoton mun kawo muku cewa Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin karin wasu mutane da za su zama cikin masu bashi shawara.

Kamar yadda The Cable ta rahoto shugaban kasar ya zabi Hadiza Bala Usman, tsohuwar shugaban NPA a matsayin wacce za ta rika bashi shawara kan tsare-tsare.

Sai kuma Hannatu Musa Musawa a matsayin mai bada shawara kan al'adu da nishadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164