Rikicin PDP: Sabuwar Rigima Ta Barke a Bayan Tsagin Wike Ya Yi Nasara Kan Atiku a Wata Yarjejeniya
- Tsagin Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Rivers a PDP, ya yi nasara akan tsagin Atiku Abubakar a majalisar wakilai
- An tattaro cewa Kingsley Chinda, wani na hannun daman Wike, an zaɓe shi a matsayin ɗan takarar PDP a kujerar shugaban marasa rinjaye na majalisar
- Zaɓin Chinda dai bai yi wa shugabannin PDP daɗi ba amma zaɓin Atiku Abubakar, Oluwole Oke ya janye daga takarar
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ƙara samu kanta cikin wani halin ƙaƙanikayi bayan sabuwar rigima ta ɓarke a tsakanin tsagin Atiku Abubakar, da na Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Rivers.
Sabuwar rigimar ta ɓarke ne a dalilin goyon bayan Kingsley Chinda, wani babban na hannun daman Wike a muƙamin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai da ƴan jam'iyyar PDP suka yi.
A cewar rahoton The Nation, Chinda ya zama ɗan takarar PDP ne ba tare da wani abokin hamayya ba a lokacin wani taro da ƴan majalisun jam'iyyar suka gudanar a birnin tarayya Abuja, a ranar Juma'a, 16 ga watan Yunin 2023.
Ɗan takarar Atiku ya janyewa zaɓin Wike a muƙamin shugaban marasa rinjaye
An samo cewa Oluwole Oke daga jihar Osun shine zaɓin tsagin Atiku akan muƙamin amma ɗan majalisar ya janye daga takarar
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasu daga cikin ƙusoshin jam'iyyar PDP waɗanda har yanzu basu yafewa tsohon gwamnan da muƙarrabansa ba kan ƙin bayar da haɗin kai a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, basu ji daɗin zaɓin da aka yi wa Chinda ba.
Tun da farko, kakakin jam'iyyar PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya yi kiran da ayi watsi da rahotannin da ke cewa an zaɓi wani a matsayin shine ɗan takarar jam'iyyar a muƙamin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai.
Hukuncin Da Ya Dace PDP Ta Yi Wa Wike
A wani labarin kuma, wani jigon jam'iyyar APC ya goyi bayan jam'iyyar PDP da ta dakatar da tsohon gwamna Wike kan cin dunduniyarta da ya yi.
Eze Chukuwemeka Eze ya ce jam'iyyar yakamata ta dakatar da tsohon gwamnan idan har tana son ta dawo da ƙimarta.
Asali: Legit.ng