“Ni Dan Kwankwasiyya Ne Amma Gina Kano Ya Kamata Ayi Ba Rusa Kano Ba” – Ali Madagwal
- Jarumin barkwanci a masana’antar Kannywood, Aliyu Muhammad Idris wanda aka fi sani da Ali Artwork ko Madagwal, ya magantu a kan rusau da Abba Gida-Gida ke yi a jihar Kano
- Madagwal ya ce shi dan Kwankwasiyya ne amma sam wannan mataki na rusau da gwamnatin Kano ta dauka bai dace ba
- Jarumin ya ce shi zai ba Abba Kabbir Yusuf aikin yi idan har bai san abun da zai yi ba sai rusau
Fitaccen jarumin barkwanci Aliyu Muhammad Idris wanda yafi shahara da sunan Madagwal, ya soki shirin rusau da gwamnatin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida take yi a jihar Kano.
Jarumin ya bayyana cewa babban abun da jihar Kano ke bukata a yanzu shine yadda za a ci gaba da ginata ba wai a rusa ta ba, kamar yadda ya bayyana cewa gwamnatin Abba Ganduje ta yi aiki idan har maganar gaskiya ake so.
Idan Abba bai da aiki ya zo ni zan ba shi aiki, Ali Madagwal
Madagwal ya cewa idan har Abba bai da aikin yi ne yasa yake rusau toh ya zo shi zai ba shi aiki, inda ya ce al'ummar kauyuka na matukar bukatar dauki domin suna cikin hali na ha'u'la'i.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma zargi sabon gwamnan da kokarin koyar da siyasar gaba inda ya ce an ci gaba yanzu ba a irin wannan siyasar sai kokarin yadda za a zauna lafiya da ciyar da kasa gaba.
Har wayau ya ce jagoran Kwankwasiyya wanda shine ubangidan Abba gida-gida, Sanata Rabiu Kwankwaso bai koyar da irin wannan hali da sabon gwamnan ke nunawa ba, yana mai cewa Kwankwaso ya zauna lafiya da abokan adawarsa a siyasa, ciki harda Ganduje.
Ga wani bangare na jawabinsa a hirarsa da Freedom radio:
"Ganduje ya yi aiki, Kwankwaso ya yi aiki, idan Abba bai da aikin da zai yi wa jihar Kano ba sai rushe-rushe toh ni Ali Madagwal zan ba shi aiki. Akwai aikace-aikace barkatai, muna da kananan hukumomi 44 a jihar Kano kuma dukkansu kowanne sun bayar da goyon baya wajen zaben Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano musamman ma makwabtanmu kauyuka.
"A matsayina kamar yadda nake fada kullun ni dan Kwankwasiyya ne kuma abun da mai girma jagora ya koyar da mu shine duk inda aka ga ba daidai ba ayi magana. Ni abun da nake gani gwamnatin jihar Kano wannan rushe-rushen da take yi, Kano dai Mallam Ibrahim Shekarau ya yi aiki, Ganduje ya yi aiki, Kwankwaso ya yi aiki.
"Akwai aikace-aikace da ya kamata ace ni ganau ne ba jiyau ba akwai kauyukan da ruwan sha sai sun yi tafiyar kilomita 10, 5 suke nemo ta."
Ga cikakken jawabin nasa a kasa:
Rusau a Kano: APC ta yi raddi ga Abba Gida-Gida
A wani labarin kuma, Legit.ng ta kawo a baya cewa an gargadi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a kan lalata ayyukan da magajinsa, Abdullahi Umar Ganduje ya bari da sunan rusa gine-gine da basa bisa ka'ida a jihar.
Cikin kasa da makonni da kama aiki, gwamnan ya shiga aikin rusa gine-ginen da basa bisa ka'ida da kudadensu ya kai biliyoyin naira
Asali: Legit.ng