Sabon Dan Majalisa Ya Samu Nasarar Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Imo
- Sabon ɗan majalisa, Chike Olemgbe, ya samu nasarar zama kakakin majalisar dokokin jihar Imo da aka rantsar ranar Jumu'a
- Honorabul Olemgbe, ɗan kimanin shekara 40 a duniya ya ci zaɓe ba tare da hamayya ba yayin rantsar ɗa majalisa ta 10
- Ya yi alkawarin cewa majalisar da zai jagoranta zata haɗa hannu da ɓangaren zartarwa domin amfanin mutanen jihar Imo
Imo State - Matashi ɗan kimanin shekara 40 a duniya, Honorabul Chike Olemgbe, ya samu nasarar lashe zaɓen kakakin majalisar dokokin jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Olemgbe, sabon ɗan majalisa a karon farko wanda zai wakilci mazaɓar Ihitte/Uboma, ya yi nasarar zama sabon kakaki ba tare da hamayya ba ranar Jumu'a.
Punch ta rahoto cewa mambobi sun kaɗa wa ɗan majalisar kuri'unsu yayin rantsar da majalisar dokoki ta 10 a Owerri, babban birnin Imo ranar 16 ga watan Yuni, 2023.
Wasu bayanai sun nuna cewa sabon kakakin majalisar bai jima da sauka daga matsayin shugaban ƙaramar hukumar Ihitte/Uboma na riƙo ba a jihar Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda matashin ya samu nasarar zama kakaki
Mamba mai wakiltar mazaɓar Ideato ta kudu, Vitalis Azodo, ne ya fara tsayar da Olemgbe a matsayin ɗan takarar da ya cancanci jagorantar majalisa ta 10, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Ba tare da ɓata lokaci ba ɗan majalisa mai wakiltar Mazaɓar Owerri Municipal, Ugochukwu Obodo, ya goyi bayansa, saura suka biyo baya suka kaɗa masa kuri'u.
Bayan nan ne magatakardan majalisar, Chinelo Emeghara, ya rantsar da sabon kakakin majalisar saboda babu wani da ya sake tsayawa takara.
Haka nan kuma tsohon kakakin majalisar dokokin Imo wanda ya sauka, Amara Iwuanyanwu, ya sake komawa a matsayin mataimakin kakaki ba tare da hamayya ba.
A jawabinsa, sabon shugaban majalisar ya sha alwashin aiki kafaɗa da kafaɗa da ɓangaren zartarwa domin shayar da mutane romon demokuraɗiyya a faɗin jihar.
Jerin Ministoci da Mukarraban Buhari Da Ya Kamata Tinubu Ya Kamo Su Yi Bayani
A wani labarin kuma Gudaji Kazauna ya fallasa sunayen manyan ƙusoshin gwamnatin Buhari daya kamata shugaba Tinubu ya damƙe su yi bayani.
Kazaure, ya ce matuƙar dagaske ana son farfaɗo da tattalin arziki, ya kamata shugaba Bola Tinubu, ya sa a kama waɗan nan mutanen.
Asali: Legit.ng